(26) Waɗanda suka kyautata yi, sunã da abu mai kyãwo kuma da ƙari, wata ƙũra bã ta rufe fuskõkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sunã madawwama a cikinta.
(27) Kuma waɗanda suka yi tsirfar mũnanan ayyuka, sakamakon mummuna da kamarsa yake, kuma ƙasƙanci yanã rufe su. Bã su da wani matsari daga Allah, kamar an rufe fuskokinsu da guntãyen ƙirãruwa daga dare mai duhu. Waɗannan ne abõkan wuta, sunã madawwama a cikinta.
(28) Kuma a rãnar da Muke tãra su gabã ɗaya, sa'an nan kuma Mu ce wa waɗanda suka yi shirki, "Ku kãma matsayinku, kũ da abũbuwan shirkĩnku." Sa'an nan Mu rarrabe a tsakãninsu, kuma abũbuwan shirkinsu su ce: "Bã mũ kuka kasance kunã bauta wa ba."
(29) "To, kuma Allah Yã isa zama shaida a tsakãninmu da tsakãninku. Haƙĩƙa mun kasance ba mu san kõme ba na bautãwarku a gare mu!"
(30) A can ne kõwane rai yake jarraba abin da ya bãyar bãshi, kuma aka mayar da su zuwa ga Allah, Majiɓincinsu Tabbatacce kuma, abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace musu.
(31) Ka ce: "Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?" To, zã su ce: "Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?"
(32) To, Wancan ne Allah, Ubangijinku Tobbatacce. To, mẽne ne a bãyan gaskiya fãce ɓãta? To, yãya ake karkatar da ku?
(33) Kamar wancan ne kalmar Ubangijinka, ta tabbata a kan waɗanda suka yi fãsiƙanci, cẽwa haƙĩƙa sũ, bã zã su yi ĩmãni ba.