(38) A can ne Zakariyya ya rõki Ubangijinsa, ya ce: "Ya Ubangijina! Ka bã ni zuriyya mai kyau daga gunKa. Lalle ne Kai Mai jin addu'a Kake."
(39) Sai malã'iku suka kirãye shi, alhãli kuwa shĩ yanã tsaye yana salla a cikin masallãci. (Suka ce), "Lalle ne Allah yana bã ka bushãra da Yahaya, alhãli yana mai gaskatãwar wata kalma daga Allah, kuma shugaba, kuma tsarkakke kuma annabi daga sãlihai."
(40) Ya ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai sãmu a gare ni, alhãli kuwa, lalle tsũfa ya sãme ni, kuma mãtãta bakarãriya ce?" Allah ya ce, "Kamar hakan ne, Allah yana aikata abin da Yake so."
(41) Ya ce: "Yã Ubangijinã! Ka sanya mini wata alãma!" (Allah) Ya ce "Alãmarka ita ce ba zã ka iya yi wa mutãne magana ba har yini uku face da ishãra. Sai ka ambaci Ubangijinka da yawa. Kuma ka yi tasbĩhi da marece da sãfe."
(42) Kuma a lõkacin da malã'iku suka ce: "Ya Maryamu! Lalle ne, Allah Ya zãɓe ki, kuma Ya tsarkake ki, kuma Ya zaɓe ki a kan mãtan tãlikai."
(43) "Yã Maryamu! Ki yi ƙanƙan da kai ga Ubangijinki, kuma ki yi sujada, kuma ki yi rukũ'i tãre da mãsu rukũ'i."
(44) Wannan yana daga lãbarun gaibi, Munã yin wahayinsa zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance ba a wurinsu a lõkacin da suke jẽfa alƙalumansu (domin ƙuri'a) wãne ne zai yi rẽnon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin da suke ta yin husũma.
(45) A lõkacin da malã'iku suka ce "Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki bushãra da wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a dũniya da Lãhira kuma daga Makusanta.