النور   سورة  : An-Noor


سورة Sura   النور   An-Noor
۞ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّبِعُوا خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ ۚ وَمَن يَتَّبِعْ خُطُوَاتِ الشَّيْطَانِ فَإِنَّهُ يَأْمُرُ بِالْفَحْشَاءِ وَالْمُنكَرِ ۚ وَلَوْلَا فَضْلُ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ مَا زَكَىٰ مِنكُم مِّنْ أَحَدٍ أَبَدًا وَلَٰكِنَّ اللَّهَ يُزَكِّي مَن يَشَاءُ ۗ وَاللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ (21) وَلَا يَأْتَلِ أُولُو الْفَضْلِ مِنكُمْ وَالسَّعَةِ أَن يُؤْتُوا أُولِي الْقُرْبَىٰ وَالْمَسَاكِينَ وَالْمُهَاجِرِينَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ ۖ وَلْيَعْفُوا وَلْيَصْفَحُوا ۗ أَلَا تُحِبُّونَ أَن يَغْفِرَ اللَّهُ لَكُمْ ۗ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ (22) إِنَّ الَّذِينَ يَرْمُونَ الْمُحْصَنَاتِ الْغَافِلَاتِ الْمُؤْمِنَاتِ لُعِنُوا فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ (23) يَوْمَ تَشْهَدُ عَلَيْهِمْ أَلْسِنَتُهُمْ وَأَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُم بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (24) يَوْمَئِذٍ يُوَفِّيهِمُ اللَّهُ دِينَهُمُ الْحَقَّ وَيَعْلَمُونَ أَنَّ اللَّهَ هُوَ الْحَقُّ الْمُبِينُ (25) الْخَبِيثَاتُ لِلْخَبِيثِينَ وَالْخَبِيثُونَ لِلْخَبِيثَاتِ ۖ وَالطَّيِّبَاتُ لِلطَّيِّبِينَ وَالطَّيِّبُونَ لِلطَّيِّبَاتِ ۚ أُولَٰئِكَ مُبَرَّءُونَ مِمَّا يَقُولُونَ ۖ لَهُم مَّغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ (26) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَدْخُلُوا بُيُوتًا غَيْرَ بُيُوتِكُمْ حَتَّىٰ تَسْتَأْنِسُوا وَتُسَلِّمُوا عَلَىٰ أَهْلِهَا ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ (27)
الصفحة Page 352
(21) Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni, kada ku bi hanyõyin Shaiɗan. Kuma wanda ke bin hanyõyin Shaiɗan, to, lalle ne shi, yanã umurni da yin alfãsha da abin da ba a sani ba, kuma bã dõmin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, bãbu wani mutum daga gare ku da zai tsarkaka har abada, kuma amma Allah Yanã tsarkake wanda Yake so kuma Allah Mai ji ne, Masani.
(22) Kuma kada ma'abũta falala daga gare ku da mawadãta su rantse ga rashin su bãyar da alhẽri ga ma'abũta zumunta da miskĩnai da muhãjirai, a cikin hanyar Allah. Kuma su yãfe, kuma su kau da kai. shin, bã ku son Allah Ya gãfarta muku, alhãli Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?
(23) Lalle ne waɗannan da suke jĩfar mãtã mãsu kãmun kai gãfilai mũminai, an la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma sunãda azãba mai girma.
(24) A rãnar da harsunansu da hannãyensu, da ƙafãfunsu suke bãyar da shaida a kansu, game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
(25) a rãnar dl Allah Yake cika musu sakamakonsu tabbatacce kuma sunã sanin (cẽwa) lalle Allah, Shi ne Gaskiya bayyananna.
(26) Miyãgun mãtã dõmin miyagun maza suke, kuma miyãgun maza dõmin miyãgun mãtã suke kuma tsarkãkan mãtã dõmin tsarkãkan maza suke kuma tsarkãkan maza dõmin tsarkãkan mãtã suke. waɗancan sũ ne waɗanda ake barrantãwa daga abin da (mãsu ƙazafi) suke faɗa kuma sunã da gãfara da arziki na karimci.
(27) Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku shiga gidãje waɗanda bã gidãjenku ba sai kun sãmi izni, kuma kun yi sallama a kan ma'abũtansu. Wannan ne mafi alhẽri gare ku, tsammaninku, zã ku tuna.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022