التوبة   سورة  : At-Tawba


سورة Sura   التوبة   At-Tawba
لَقَدِ ابْتَغَوُا الْفِتْنَةَ مِن قَبْلُ وَقَلَّبُوا لَكَ الْأُمُورَ حَتَّىٰ جَاءَ الْحَقُّ وَظَهَرَ أَمْرُ اللَّهِ وَهُمْ كَارِهُونَ (48) وَمِنْهُم مَّن يَقُولُ ائْذَن لِّي وَلَا تَفْتِنِّي ۚ أَلَا فِي الْفِتْنَةِ سَقَطُوا ۗ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةٌ بِالْكَافِرِينَ (49) إِن تُصِبْكَ حَسَنَةٌ تَسُؤْهُمْ ۖ وَإِن تُصِبْكَ مُصِيبَةٌ يَقُولُوا قَدْ أَخَذْنَا أَمْرَنَا مِن قَبْلُ وَيَتَوَلَّوا وَّهُمْ فَرِحُونَ (50) قُل لَّن يُصِيبَنَا إِلَّا مَا كَتَبَ اللَّهُ لَنَا هُوَ مَوْلَانَا ۚ وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ (51) قُلْ هَلْ تَرَبَّصُونَ بِنَا إِلَّا إِحْدَى الْحُسْنَيَيْنِ ۖ وَنَحْنُ نَتَرَبَّصُ بِكُمْ أَن يُصِيبَكُمُ اللَّهُ بِعَذَابٍ مِّنْ عِندِهِ أَوْ بِأَيْدِينَا ۖ فَتَرَبَّصُوا إِنَّا مَعَكُم مُّتَرَبِّصُونَ (52) قُلْ أَنفِقُوا طَوْعًا أَوْ كَرْهًا لَّن يُتَقَبَّلَ مِنكُمْ ۖ إِنَّكُمْ كُنتُمْ قَوْمًا فَاسِقِينَ (53) وَمَا مَنَعَهُمْ أَن تُقْبَلَ مِنْهُمْ نَفَقَاتُهُمْ إِلَّا أَنَّهُمْ كَفَرُوا بِاللَّهِ وَبِرَسُولِهِ وَلَا يَأْتُونَ الصَّلَاةَ إِلَّا وَهُمْ كُسَالَىٰ وَلَا يُنفِقُونَ إِلَّا وَهُمْ كَارِهُونَ (54)
الصفحة Page 195
(48) Kuma lalle ne, haƙĩƙa sun nẽmi fitina daga gabãni, kuma, suka jũya maka al'amari, har gaskiya ta zo, kuma umurnin Allah Ya bayyana, alhãli sunã mãsu ƙyãma,
(49) Kuma daga cikinsu akwai mai cẽwa, "Ka yi mini izinin zama, kuma kada ka fitine ni." To, a cikin fitinar suka fãɗa. Kuma lalle ne Jahannama, haƙĩƙa, mai ƙẽwayẽwa ce ga kãfirai.
(50) Idan wani alhẽri ya sãme ka, zai ɓãta musu rai, kuma idan wata masifa ta sãme ka sai su ce: "Haƙĩƙa, mun riƙe al'amarinmu daga gabãni."Kuma sujũya, alhãli kuwa sunã mãsu farin ciki.
(51) Ka ce: "Bãbu abin da yake sãmun mu fãce abin da Allah Ya rubũta sahõda mu. Shĩ ne Majiɓincinmu. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara."
(52) Ka ce: "Shin, kunã dãko ne da mu? Fãce dai da ɗayan abũbuwan biyu mãsu kyau, alhãli kuwa mũ, munã dãko da ku, AllahYa sãme ku da wata azãba daga gare Shi, kõ kuwa da hannayenmu. To, ku yi dãko. Lalle ne mũ, tãre da ku mãsu dãkon ne."
(53) Ka ce: "Ku ciyar a kan yarda kõ kuwa a kan tĩlas. Bã zã a karɓa daga gare ku ba. Lalle ne kũ, kun kasance mutãne fãsiƙai."
(54) Kuma bãbu abin da ya hana a karɓi ciyarwarsu daga gare su fãce dõmin sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa, kuma bã su zuwa ga salla fãce Luma sunã mãsu kasãla, kuma bã su ciyarwa fãce sunã mãsu ƙyãma.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022