التين   سورة  : At-Tin


سورة Sura   التين   At-Tin
التين At-Tin
بِّسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ وَالتِّينِ وَالزَّيْتُونِ (1) وَطُورِ سِينِينَ (2) وَهَٰذَا الْبَلَدِ الْأَمِينِ (3) لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ فِي أَحْسَنِ تَقْوِيمٍ (4) ثُمَّ رَدَدْنَاهُ أَسْفَلَ سَافِلِينَ (5) إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَلَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ (6) فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعْدُ بِالدِّينِ (7) أَلَيْسَ اللَّهُ بِأَحْكَمِ الْحَاكِمِينَ (8)
العلق Al-Alaq
اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ (1) خَلَقَ الْإِنسَانَ مِنْ عَلَقٍ (2) اقْرَأْ وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ (3) الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ (4) عَلَّمَ الْإِنسَانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ (5) كَلَّا إِنَّ الْإِنسَانَ لَيَطْغَىٰ (6) أَن رَّآهُ اسْتَغْنَىٰ (7) إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ الرُّجْعَىٰ (8) أَرَأَيْتَ الَّذِي يَنْهَىٰ (9) عَبْدًا إِذَا صَلَّىٰ (10) أَرَأَيْتَ إِن كَانَ عَلَى الْهُدَىٰ (11) أَوْ أَمَرَ بِالتَّقْوَىٰ (12) أَرَأَيْتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ (13) أَلَمْ يَعْلَم بِأَنَّ اللَّهَ يَرَىٰ (14) كَلَّا لَئِن لَّمْ يَنتَهِ لَنَسْفَعًا بِالنَّاصِيَةِ (15) نَاصِيَةٍ كَاذِبَةٍ خَاطِئَةٍ (16) فَلْيَدْعُ نَادِيَهُ (17) سَنَدْعُ الزَّبَانِيَةَ (18) كَلَّا لَا تُطِعْهُ وَاسْجُدْ وَاقْتَرِب ۩ (19)
الصفحة Page 597
التين At-Tin
(1) Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.
(2) Da Dũr Sĩnĩna.
(3) Da wannan gari amintacce.
(4) Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
(5) Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
(6) Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
(7) To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
(8) Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?
العلق Al-Alaq
(1) Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
(2) Ya hahitta mutum daga gudan jini.
(3) Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.
(4) Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.
(5) Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.
(6) A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).
(7) Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.
(8) Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
(9) Shin, kã ga wanda ke hana.
(10) Bãwã idan yã yi salla?
(11) Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?
(12) Ko ya yi umurni da taƙawa?
(13) Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?
(14) Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?
(15) A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.
(16) Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.
(17) Sai ya kirayi ƙungiyarsa.
(18) Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).
(19) A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022