(74) Kuma a lõkacin da Ibrãhĩma ya ce wa ubansa Ãzara: "Shin, kanã riƙon gumãka abũbuwan bautãwa? Lalle nĩ, inã ganin ka kai damutã- nenka, a cikin ɓata bayyananniya."
(75) Kuma kamar wancan ne, Muke nũna wa Ibrãhĩma mulkin sammai da ƙasa, kuma dõmin ya kasance daga mãsu yaƙĩni.
(76) To, a lõkacin da dare ya rufe a kansa, ya ga wani taurãro, ya ce: "Wannan ne, ubangijina?" Sa'an nan a lõkacin da ya faɗi, ya ce: "Ba ni son mãsu fãɗuwa."
(77) Sa'an nan a lõkacin da ya ga watã yanã mai bayyana, ya ce: "Wannan ne Ubangijina?" Sa'an nan a lõkacin da ya fãɗi, ya ce: "Lalle ne idan Ubangijina bai shiryar da ni ba, haƙĩƙa, inã kasancẽwa daga mutãne ɓatattu."
(78) Sa'an nan a lõkacin da ya ga rãnã tanã bayyana, ya ce: "Wannan shĩ ne Ubangijina, wannan ne mafi girma?" Sa'an nan a lõkacin da ta fãɗi, ya ce: "Ya mutãnena! Lalle ne ni barrantacce nake daga abin da kuke yi na shirki."
(79) "Lalle ne nĩ, na fuskantar da fuskata ga wanda, Ya ƙãga halittar sammai da ƙasa, inã mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bã ni cikin mãsu shirki."
(80) Kuma mutãnensa suka yi musu da shi. Ya ce: "Shin kunã musu da ni a cikin sha'anin Allah, alhãli kuwa Yã shiryai da ni? Kuma bã ni tsõron abin da kuke yin shirki da shi, fãce idan Ubangijina Yã so wani abu. Ubangijina Ya yalwaci dukkan kõme da ilmi. Shin, ba zã ku yi tunãni ba?"
(81) "Kuma yãyã nake jin tsõron abin da kuka yi shirki da shi, kuma ba ku tsõron cẽwa lalle ne kũ, kun yi shirki da Allah, abin da (Allah) bai saukar da wata hujja ba game da shi? To, wane ɓangare daga sãshen biyu ne mafi cancanta da aminci, idan kun kasance kunã sani?"