المؤمنون   سورة  : Al-Muminoon


سورة Sura   المؤمنون   Al-Muminoon
فَإِذَا اسْتَوَيْتَ أَنتَ وَمَن مَّعَكَ عَلَى الْفُلْكِ فَقُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي نَجَّانَا مِنَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ (28) وَقُل رَّبِّ أَنزِلْنِي مُنزَلًا مُّبَارَكًا وَأَنتَ خَيْرُ الْمُنزِلِينَ (29) إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ وَإِن كُنَّا لَمُبْتَلِينَ (30) ثُمَّ أَنشَأْنَا مِن بَعْدِهِمْ قَرْنًا آخَرِينَ (31) فَأَرْسَلْنَا فِيهِمْ رَسُولًا مِّنْهُمْ أَنِ اعْبُدُوا اللَّهَ مَا لَكُم مِّنْ إِلَٰهٍ غَيْرُهُ ۖ أَفَلَا تَتَّقُونَ (32) وَقَالَ الْمَلَأُ مِن قَوْمِهِ الَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِلِقَاءِ الْآخِرَةِ وَأَتْرَفْنَاهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا مَا هَٰذَا إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ يَأْكُلُ مِمَّا تَأْكُلُونَ مِنْهُ وَيَشْرَبُ مِمَّا تَشْرَبُونَ (33) وَلَئِنْ أَطَعْتُم بَشَرًا مِّثْلَكُمْ إِنَّكُمْ إِذًا لَّخَاسِرُونَ (34) أَيَعِدُكُمْ أَنَّكُمْ إِذَا مِتُّمْ وَكُنتُمْ تُرَابًا وَعِظَامًا أَنَّكُم مُّخْرَجُونَ (35) ۞ هَيْهَاتَ هَيْهَاتَ لِمَا تُوعَدُونَ (36) إِنْ هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا الدُّنْيَا نَمُوتُ وَنَحْيَا وَمَا نَحْنُ بِمَبْعُوثِينَ (37) إِنْ هُوَ إِلَّا رَجُلٌ افْتَرَىٰ عَلَى اللَّهِ كَذِبًا وَمَا نَحْنُ لَهُ بِمُؤْمِنِينَ (38) قَالَ رَبِّ انصُرْنِي بِمَا كَذَّبُونِ (39) قَالَ عَمَّا قَلِيلٍ لَّيُصْبِحُنَّ نَادِمِينَ (40) فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ بِالْحَقِّ فَجَعَلْنَاهُمْ غُثَاءً ۚ فَبُعْدًا لِّلْقَوْمِ الظَّالِمِينَ (41) ثُمَّ أَنشَأْنَا مِن بَعْدِهِمْ قُرُونًا آخَرِينَ (42)
الصفحة Page 344
(28) "Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai."
(29) "Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa.'"
(30) Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙẽƙa' Mãsu jarrabãwa.
(31) Sa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu.
(32) Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba?"
(33) Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: "Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã."
(34) "Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne."
(35) "Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da ɓasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne?"
(36) "Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi."
(37) "Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
(38) "Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba."
(39) Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni."
(40) Ya ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma."
(41) Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai!
(42) Sa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022