الشرح   سورة  : Ash-Sharh


سورة Sura   الشرح   Ash-Sharh
لَا يَصْلَاهَا إِلَّا الْأَشْقَى (15) الَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ (16) وَسَيُجَنَّبُهَا الْأَتْقَى (17) الَّذِي يُؤْتِي مَالَهُ يَتَزَكَّىٰ (18) وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُ مِن نِّعْمَةٍ تُجْزَىٰ (19) إِلَّا ابْتِغَاءَ وَجْهِ رَبِّهِ الْأَعْلَىٰ (20) وَلَسَوْفَ يَرْضَىٰ (21)
الضحى Ad-Dhuhaa
وَالضُّحَىٰ (1) وَاللَّيْلِ إِذَا سَجَىٰ (2) مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ (3) وَلَلْآخِرَةُ خَيْرٌ لَّكَ مِنَ الْأُولَىٰ (4) وَلَسَوْفَ يُعْطِيكَ رَبُّكَ فَتَرْضَىٰ (5) أَلَمْ يَجِدْكَ يَتِيمًا فَآوَىٰ (6) وَوَجَدَكَ ضَالًّا فَهَدَىٰ (7) وَوَجَدَكَ عَائِلًا فَأَغْنَىٰ (8) فَأَمَّا الْيَتِيمَ فَلَا تَقْهَرْ (9) وَأَمَّا السَّائِلَ فَلَا تَنْهَرْ (10) وَأَمَّا بِنِعْمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثْ (11)
الشرح Ash-Sharh
أَلَمْ نَشْرَحْ لَكَ صَدْرَكَ (1) وَوَضَعْنَا عَنكَ وِزْرَكَ (2) الَّذِي أَنقَضَ ظَهْرَكَ (3) وَرَفَعْنَا لَكَ ذِكْرَكَ (4) فَإِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا (5) إِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا (6) فَإِذَا فَرَغْتَ فَانصَبْ (7) وَإِلَىٰ رَبِّكَ فَارْغَب (8)
الصفحة Page 596
(15) Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa.
(16) Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya.
(17) Kuma mafi taƙawa zai nisance ta.
(18) Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka.
(19) Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta.
(20) Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka.
(21) To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi).
الضحى Ad-Dhuhaa
(1) Inã rantsuwa da hantsi.
(2) Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
(3) Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
(4) Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
(5) Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
(6) Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
(7) Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
(8) Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
(9) Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
(10) Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
(11) Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).
الشرح Ash-Sharh
(1) Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
(2) Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.
(3) Wanda ya nauyayi bãyanka?
(4) Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
(5) To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
(6) Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
(7) Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
(8) Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022