(88) Mashawarta waɗanda suka kangare daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, Munã fitar da kai, Yã Shu'aibu, kai da waɗanda suka yi Ĩmãni tãre da kai, daga alƙaryarmu; kõ kuwa lalle ku kõmo a cikin addininmu." Ya ce: "Ashe! Kuma kõ dã mun kasance mãsu ƙĩ?"
(89) "Lalle ne mun ƙirƙira ƙarya ga Allah idan mun kõma a cikin addininku a bãyan lõkacin da Allah ya tsĩrar da mu daga gare shi, kuma bã ya kasancewa a gare mu, mu kõma a cikinsa, fãce idan Al1ah, Ubangijinmu Ya so. Ubangijinmu Yã yalwaci dukan kõme ga ilmi. Ga Allah muka dõgara. Yã Ubangijinmu! Ka yi hukunci a tsakãninmu da tsakanin mutãnenmu da gaskiya, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu hukunci."
(90) Kuma mashawarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Lalle ne, idan kun bi Shu'aibu haƙĩƙa kũ, a lõkacin nan, mãsu hasãra ne."
(91) Sai tsãwa ta kãma su, sabõda haka suka wãyi gari, a cikin gidansu, sunã guggurfãne.
(92) Waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu kamar ba su zauna ba a cikinta, waɗanda suka ƙaryata Shu'aibu, sun kasance sũ nemãsu hasãra!
(93) Sai ya jũya daga barinsu, kuma ya ce: "Yã mutãnena! Haƙĩƙa, nã iyar muku da sãƙonnin Ubangijina, kuma nã yi muku nasĩha! To, yãya zan yi baƙin ciki a kan mutãne kãfirai?"
(94) Kuma ba Mu aika wani Annabi a cikin wata alƙarya ba, fãce Mun kãma mutãnenta da azãba da cũta, tsammãninsu sunã yin ƙasƙantar da kai.
(95) Sa'an nan kuma Muka musanya mai kyau a matsayin mummũna, har su yi yawa, kuma su ce: "Cũta da azãba sun shãfi ubanninmu." (sai su kõma wa kãfirci). Sai Mu kãmã su kwatsam! alhãli kuwa sũ, bã su sansancẽwa."