الهمزة   سورة  : Al-Humaza


سورة Sura   الهمزة   Al-Humaza
الصفحة Page 601
العصر Al-Asr
(1) Ina rantsuwa da zãmani.
(2) Lalle ne mutum yana a cikin hasara.
(3) Fãce waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka yi wa juna wasiyya da bin gaskiya, kuma suka yi wa juna wasiyya da yin haƙuri (su kam, basu cikin hasara).
الهمزة Al-Humaza
(1) Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa).
(2) Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa.
(3) Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi.
(4) A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama.
(5) Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama?
(6) Wutar Allah ce wadda ake hurawa.
(7) Wadda take lẽƙãwa a kan zukata.
(8) Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu.
(9) A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu.
الفيل Al-Fil
(1) Ashe, ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ga mutanen giwa ba?
(2) Ashe, bai sanya kaidinsu a cikin ɓata ba?
(3) Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.
(4) Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
(5) Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022