(32) Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?"
(33) Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja."
(34) Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne."
(35) "Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako."
(36) Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su."
(37) Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri."
(38) "Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne."
(39) Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya."
(40) "Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake."
(41) Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici."
(42) "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu."
(43) Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'a1kawartarsu gabã ɗaya.
(44) Tanã da ƙõfõfi bakwai, ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe.
(45) Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa.
(46) "Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu."
(47) Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã.
(48) Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikinta ba.
(49) Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai.
(50) Kuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi.
(51) Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm.