(118) Kuma dã Ubangijinka Ya so, dã Yã sanya mutãne al'umma guda. Kuma bã zã su gushe ba sunã mãsu sãɓã wa jũna.
(119) Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama, kuma dõmin wannan ne Ya halicce su. Kuma kalmar "Ubangijinka" Lalle ne zã Ni cika Jahannama da aljannu da mutãne gaba ɗaya" ta cika.
(120) Kuma dũbi dai Munã bã da lãbãri a gare ka daga lãbarun Manzanni, abin da Muke tabbatar da zuciyarka da shi. Kuma gaskiya ta zo maka a cikin wannan da wa'azi da tunãtarwã ga mãsu ĩmãni.
(121) kuma kace wa waɗanda bã su yin ĩmãni, "Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle mũ mãsu aiki ne.
(122) "Kuma ku yi Jiran dãko, lalle mu mãsu Jiran dãko ne."
(123) Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake. Kuma zuwa gare Shi ake mayar da dukan al'amari. Sabõda haka ku bauta Masa kuma ku dõgara a kanSa. Kuma Ubangijinka bai zama Mai gafala daga abin da kuke aikatãwa ba.
يوسف Yusuf
(1) A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin Littãfi mai bayyanãwa ne.
(2) Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yanã abin karantãwa na Lãrabci; tsammãninkũ, kunã hankalta.
(3) Mũ, Munã bãyar da lãbãri a gare ka, mafi kyãwon lãbãri ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ãni zuwa gare ka. Kuma lalle ne kã kasance a gabãninsa, haƙĩƙa, daga gafalallu.
(4) A lõkacin da Yũsufu ya ce wa ubansa, "Yã bãba! Lalle ne nĩ, nã ga taurãri gõma shã ɗaya, da rãnã da watã. Na gan su sunã mãsu sujada a gare ni."