مريم   سورة  : Maryam


سورة Sura   مريم   Maryam
أَفَرَأَيْتَ الَّذِي كَفَرَ بِآيَاتِنَا وَقَالَ لَأُوتَيَنَّ مَالًا وَوَلَدًا (77) أَطَّلَعَ الْغَيْبَ أَمِ اتَّخَذَ عِندَ الرَّحْمَٰنِ عَهْدًا (78) كَلَّا ۚ سَنَكْتُبُ مَا يَقُولُ وَنَمُدُّ لَهُ مِنَ الْعَذَابِ مَدًّا (79) وَنَرِثُهُ مَا يَقُولُ وَيَأْتِينَا فَرْدًا (80) وَاتَّخَذُوا مِن دُونِ اللَّهِ آلِهَةً لِّيَكُونُوا لَهُمْ عِزًّا (81) كَلَّا ۚ سَيَكْفُرُونَ بِعِبَادَتِهِمْ وَيَكُونُونَ عَلَيْهِمْ ضِدًّا (82) أَلَمْ تَرَ أَنَّا أَرْسَلْنَا الشَّيَاطِينَ عَلَى الْكَافِرِينَ تَؤُزُّهُمْ أَزًّا (83) فَلَا تَعْجَلْ عَلَيْهِمْ ۖ إِنَّمَا نَعُدُّ لَهُمْ عَدًّا (84) يَوْمَ نَحْشُرُ الْمُتَّقِينَ إِلَى الرَّحْمَٰنِ وَفْدًا (85) وَنَسُوقُ الْمُجْرِمِينَ إِلَىٰ جَهَنَّمَ وِرْدًا (86) لَّا يَمْلِكُونَ الشَّفَاعَةَ إِلَّا مَنِ اتَّخَذَ عِندَ الرَّحْمَٰنِ عَهْدًا (87) وَقَالُوا اتَّخَذَ الرَّحْمَٰنُ وَلَدًا (88) لَّقَدْ جِئْتُمْ شَيْئًا إِدًّا (89) تَكَادُ السَّمَاوَاتُ يَتَفَطَّرْنَ مِنْهُ وَتَنشَقُّ الْأَرْضُ وَتَخِرُّ الْجِبَالُ هَدًّا (90) أَن دَعَوْا لِلرَّحْمَٰنِ وَلَدًا (91) وَمَا يَنبَغِي لِلرَّحْمَٰنِ أَن يَتَّخِذَ وَلَدًا (92) إِن كُلُّ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ إِلَّا آتِي الرَّحْمَٰنِ عَبْدًا (93) لَّقَدْ أَحْصَاهُمْ وَعَدَّهُمْ عَدًّا (94) وَكُلُّهُمْ آتِيهِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فَرْدًا (95)
الصفحة Page 311
(77) Shin, ka ga wanda ya kãfirta da ayõyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne zã a bã ni dũkiya da ɗiya?"
(78) Shin, yã tsinkãyi gaibi ne, kõ kuwa yã ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne?
(79) Ã'aha! zã mu rubũta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azãba, yalwatãwa.
(80) Kuma Mu gãde shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yanã shi kɗai.
(81) Kuma suka riƙi gumãka, baicin Allah, dõmin su kãsance mataimaka a gare su.
(82) Ã'aha! Zã su kãfirta da ibãdarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu.
(83) Shin, ba ka gani ba cẽwa Mun saki shaiɗanu a kan kãfirai sunã shũshũta su ga zunubi shũshũtãwa?
(84) Sabõda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Munã yi musu ƙidãyar ajali ne kawai, ƙidãyãwa.
(85) A rãnar da Muka tãra mãsu taƙawa zuwa ga Mai rahama sunã bãƙin girma.
(86) Kuma Munã kõra mãsu laifi zuwa Jahannama, gargaãwa.
(87) Ba su mal1akar cẽto fãce wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama.
(88) Kuma suka ce: "Mai rahama Yã riƙi ã!"
(89) Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni.
(90) Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu.
(91) Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama.
(92) Alhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã.
(93) Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã.
(94) Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya.
(95) Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar ¡iyãma yanã shi kaɗai.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022