الأنعام   سورة  : Al-An'aam


سورة Sura   الأنعام   Al-An'aam
۞ وَلَوْ أَنَّنَا نَزَّلْنَا إِلَيْهِمُ الْمَلَائِكَةَ وَكَلَّمَهُمُ الْمَوْتَىٰ وَحَشَرْنَا عَلَيْهِمْ كُلَّ شَيْءٍ قُبُلًا مَّا كَانُوا لِيُؤْمِنُوا إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ يَجْهَلُونَ (111) وَكَذَٰلِكَ جَعَلْنَا لِكُلِّ نَبِيٍّ عَدُوًّا شَيَاطِينَ الْإِنسِ وَالْجِنِّ يُوحِي بَعْضُهُمْ إِلَىٰ بَعْضٍ زُخْرُفَ الْقَوْلِ غُرُورًا ۚ وَلَوْ شَاءَ رَبُّكَ مَا فَعَلُوهُ ۖ فَذَرْهُمْ وَمَا يَفْتَرُونَ (112) وَلِتَصْغَىٰ إِلَيْهِ أَفْئِدَةُ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِالْآخِرَةِ وَلِيَرْضَوْهُ وَلِيَقْتَرِفُوا مَا هُم مُّقْتَرِفُونَ (113) أَفَغَيْرَ اللَّهِ أَبْتَغِي حَكَمًا وَهُوَ الَّذِي أَنزَلَ إِلَيْكُمُ الْكِتَابَ مُفَصَّلًا ۚ وَالَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يَعْلَمُونَ أَنَّهُ مُنَزَّلٌ مِّن رَّبِّكَ بِالْحَقِّ ۖ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ الْمُمْتَرِينَ (114) وَتَمَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ صِدْقًا وَعَدْلًا ۚ لَّا مُبَدِّلَ لِكَلِمَاتِهِ ۚ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ (115) وَإِن تُطِعْ أَكْثَرَ مَن فِي الْأَرْضِ يُضِلُّوكَ عَن سَبِيلِ اللَّهِ ۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا الظَّنَّ وَإِنْ هُمْ إِلَّا يَخْرُصُونَ (116) إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ مَن يَضِلُّ عَن سَبِيلِهِ ۖ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ (117) فَكُلُوا مِمَّا ذُكِرَ اسْمُ اللَّهِ عَلَيْهِ إِن كُنتُم بِآيَاتِهِ مُؤْمِنِينَ (118)
الصفحة Page 142
(111) Kuma dã a ce, lalle Mũ Mun saukar da Malã'iku zuwa gare su, kuma matattu suka yi musu magana, kuma Muka tãra dukkan kõme a kansu, gungu-gungu, ba su kasance sunã iya yin ĩmãni ba, sai fa idan Allah Yã so, Kuma amma mafi yawansu sunã jãhiltar haka.
(112) Kuma kamar wancan ne Muka sanya wa kõwane Annabi maƙiyi; shaiɗãnun mutãne da aljannu, sãshensu yanã yin ishãra zuwa sãshe da ƙawãtaccen zance bisa ga rũɗi. Kuma dã Ubangijinka Yã so, dã ba su aikatã shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke ƙirƙirãwa.
(113) Kuma dõmin zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba su karkata saurãrẽ zuwa gareshi, kuma dõmin su yarda da shi, kuma dõmin su kamfaci abin da suke mãsu kamfata.
(114) Shin fa, wanin Allah nake nẽma ya zama mai hukunci, alhãli kuwa Shĩ ne wanda Ya saukar muku da Littãfi abin rabẽwadaki-daki? Kuma waɗanda Muka bai wa Littãfi sunã sanin cẽwa lalleshi (Alƙur'ãni) abin saukarwa ne daga Ubangijinka, da gaskiya? Sabõda haka kada ku kasance daga mãsu shakka.
(115) Kuma kalmar Ubangijinka tã cika, tanã gaskiya da ãdalci. Babu mai musanyãwa ga kalmõminSa, kuma Shi ne Maiji, Masani.
(116) Kuma idan ka bi mafiya yawan waɗanda suke a cikin ƙasa da ɗã'a sunã ɓatar da kai daga hanyar Allah. Ba su bin kõme sai fãce ƙaddari-faɗi suke yi.
(117) Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga wanda yake ɓacẽwa daga hanyarsa kuma Shi ne mafi sani ga masu shiryuwa.
(118) Sabõda haka ku ci daga abin da aka ambaci sũnan Allah kansa, idan kun kasance mãsu ĩmãni da ãyõyinSa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022