التوبة   سورة  : At-Tawba


سورة Sura   التوبة   At-Tawba
رَضُوا بِأَن يَكُونُوا مَعَ الْخَوَالِفِ وَطُبِعَ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا يَفْقَهُونَ (87) لَٰكِنِ الرَّسُولُ وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ جَاهَدُوا بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ ۚ وَأُولَٰئِكَ لَهُمُ الْخَيْرَاتُ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ (88) أَعَدَّ اللَّهُ لَهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ ذَٰلِكَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ (89) وَجَاءَ الْمُعَذِّرُونَ مِنَ الْأَعْرَابِ لِيُؤْذَنَ لَهُمْ وَقَعَدَ الَّذِينَ كَذَبُوا اللَّهَ وَرَسُولَهُ ۚ سَيُصِيبُ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ (90) لَّيْسَ عَلَى الضُّعَفَاءِ وَلَا عَلَى الْمَرْضَىٰ وَلَا عَلَى الَّذِينَ لَا يَجِدُونَ مَا يُنفِقُونَ حَرَجٌ إِذَا نَصَحُوا لِلَّهِ وَرَسُولِهِ ۚ مَا عَلَى الْمُحْسِنِينَ مِن سَبِيلٍ ۚ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ (91) وَلَا عَلَى الَّذِينَ إِذَا مَا أَتَوْكَ لِتَحْمِلَهُمْ قُلْتَ لَا أَجِدُ مَا أَحْمِلُكُمْ عَلَيْهِ تَوَلَّوا وَّأَعْيُنُهُمْ تَفِيضُ مِنَ الدَّمْعِ حَزَنًا أَلَّا يَجِدُوا مَا يُنفِقُونَ (92) ۞ إِنَّمَا السَّبِيلُ عَلَى الَّذِينَ يَسْتَأْذِنُونَكَ وَهُمْ أَغْنِيَاءُ ۚ رَضُوا بِأَن يَكُونُوا مَعَ الْخَوَالِفِ وَطَبَعَ اللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ فَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ (93)
الصفحة Page 201
(87) Sun yarda da su kasance tãre da mãtã mãsu zama (a cikin gidãje). Kuma aka rufe a kan zukãtansu, sabõda haka, sũ, bã su fahimta.
(88) Amma Manzon Allah da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, sun yi jihãdi da dũkiyõyinsu da rãyukansu. Kuma waɗannan sunã da ayyukan alhẽri, kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara.
(89) Allah yã yi musu tattalin gidãjen Aljanna, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwamã a cikinsu. Wancan ne babban rabo mai girma.
(90) Kuma mãsu uzuri daga ƙauyãwa zuka zo dõmin a yi musu izini, kuma waɗanda suka yi wa Allah da ManzonSa ƙarya, suka yi zamansu. wata azãba mai raɗaɗi zã ta sãmi waɗanda suka kãfirta daga gare su.
(91) Bãbu laifi a kan maraunana kuma haka majinyata, kuma bãbu laifi a kan waɗanda bã su sãmun abin da suke ciyarwa idan sun yi nasĩha ga Allah da ManzonSa. Kuma bãbu wani laifi a kan mãsu kyautatãwa. Kuma Allah ne Mai gãfara, Mai tausayi.
(92) Kuma bãbu (laifi) a kan waɗanda idan sun je maka dõmin ka ɗauke su ka ce: "Bã ni da abin da nake ɗaukar ku a kansa," suka jũya alhãli kuwa idãnunsu sunã zubar da hawãye dõmin baƙin ciki cẽwa ba su sãmi abin da suke ciyarwa ba.
(93) Abin sani kawai, laifi Yanã a kan waɗanda suke nẽman izininka alhãli kuwa sũ mawadãta ne. Sun yarda su kasance tãre da mãtã mamaya (gidãje), kuma Allah Yã danne a kan zukãtansu, dõmin haka sũ, bã su gãnẽwa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022