التغابن   سورة  : At-Taghaabun


سورة Sura   التغابن   At-Taghaabun
وَالَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ خَالِدِينَ فِيهَا ۖ وَبِئْسَ الْمَصِيرُ (10) مَا أَصَابَ مِن مُّصِيبَةٍ إِلَّا بِإِذْنِ اللَّهِ ۗ وَمَن يُؤْمِن بِاللَّهِ يَهْدِ قَلْبَهُ ۚ وَاللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ (11) وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ ۚ فَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَإِنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ (12) اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ (13) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ مِنْ أَزْوَاجِكُمْ وَأَوْلَادِكُمْ عَدُوًّا لَّكُمْ فَاحْذَرُوهُمْ ۚ وَإِن تَعْفُوا وَتَصْفَحُوا وَتَغْفِرُوا فَإِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ (14) إِنَّمَا أَمْوَالُكُمْ وَأَوْلَادُكُمْ فِتْنَةٌ ۚ وَاللَّهُ عِندَهُ أَجْرٌ عَظِيمٌ (15) فَاتَّقُوا اللَّهَ مَا اسْتَطَعْتُمْ وَاسْمَعُوا وَأَطِيعُوا وَأَنفِقُوا خَيْرًا لِّأَنفُسِكُمْ ۗ وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفْسِهِ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ (16) إِن تُقْرِضُوا اللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا يُضَاعِفْهُ لَكُمْ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ۚ وَاللَّهُ شَكُورٌ حَلِيمٌ (17) عَالِمُ الْغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (18)
الصفحة Page 557
(10) Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata game da ayõyinMu, waɗannan sũne'yan wuta, sunã madawwama a cikinta. Kuma tir da makõma, ita.
(11) Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne.
(12) Kuma ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo. Sa'an nan idan kun jũya bãya, to, abin sani kawai, akwai iyarwa bayyananna a kan ManzonMu.
(13) Allah bãbu wani abin bauta wa fãce Shi. Kuma ga Allah, sai mũminai su dõgara.
(14) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
(15) Dũkiyõyinku da ɗiyanku fitina ɗai ne. Kuma Allah, a wurinSa akwai wani sakamako mai girma.
(16) Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma ku yi ɗã'ã, kuma ku ciyar, ya fi zama alhẽri gare ku. Kuma wandaya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.
(17) Idan kun bai wa Allah rance, rance mai kyau, (Allah) zai ninka shi a gare ku kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai yawan gõdiya ne, Mai haƙuri.
(18) Shĩ ne Masanin fake da bayyane, Mabuwayi, Mai hikima.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022