النور   سورة  : An-Noor


سورة Sura   النور   An-Noor
رِجَالٌ لَّا تُلْهِيهِمْ تِجَارَةٌ وَلَا بَيْعٌ عَن ذِكْرِ اللَّهِ وَإِقَامِ الصَّلَاةِ وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ ۙ يَخَافُونَ يَوْمًا تَتَقَلَّبُ فِيهِ الْقُلُوبُ وَالْأَبْصَارُ (37) لِيَجْزِيَهُمُ اللَّهُ أَحْسَنَ مَا عَمِلُوا وَيَزِيدَهُم مِّن فَضْلِهِ ۗ وَاللَّهُ يَرْزُقُ مَن يَشَاءُ بِغَيْرِ حِسَابٍ (38) وَالَّذِينَ كَفَرُوا أَعْمَالُهُمْ كَسَرَابٍ بِقِيعَةٍ يَحْسَبُهُ الظَّمْآنُ مَاءً حَتَّىٰ إِذَا جَاءَهُ لَمْ يَجِدْهُ شَيْئًا وَوَجَدَ اللَّهَ عِندَهُ فَوَفَّاهُ حِسَابَهُ ۗ وَاللَّهُ سَرِيعُ الْحِسَابِ (39) أَوْ كَظُلُمَاتٍ فِي بَحْرٍ لُّجِّيٍّ يَغْشَاهُ مَوْجٌ مِّن فَوْقِهِ مَوْجٌ مِّن فَوْقِهِ سَحَابٌ ۚ ظُلُمَاتٌ بَعْضُهَا فَوْقَ بَعْضٍ إِذَا أَخْرَجَ يَدَهُ لَمْ يَكَدْ يَرَاهَا ۗ وَمَن لَّمْ يَجْعَلِ اللَّهُ لَهُ نُورًا فَمَا لَهُ مِن نُّورٍ (40) أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ يُسَبِّحُ لَهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَالطَّيْرُ صَافَّاتٍ ۖ كُلٌّ قَدْ عَلِمَ صَلَاتَهُ وَتَسْبِيحَهُ ۗ وَاللَّهُ عَلِيمٌ بِمَا يَفْعَلُونَ (41) وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ وَإِلَى اللَّهِ الْمَصِيرُ (42) أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ يُزْجِي سَحَابًا ثُمَّ يُؤَلِّفُ بَيْنَهُ ثُمَّ يَجْعَلُهُ رُكَامًا فَتَرَى الْوَدْقَ يَخْرُجُ مِنْ خِلَالِهِ وَيُنَزِّلُ مِنَ السَّمَاءِ مِن جِبَالٍ فِيهَا مِن بَرَدٍ فَيُصِيبُ بِهِ مَن يَشَاءُ وَيَصْرِفُهُ عَن مَّن يَشَاءُ ۖ يَكَادُ سَنَا بَرْقِهِ يَذْهَبُ بِالْأَبْصَارِ (43)
الصفحة Page 355
(37) Waɗansu maza, waɗanda wani fatauci bã ya shagaltar da su, kuma sayarwa bã ta shagaltar da su daga ambaton Allah, da tsai da salla da bãyar da zakka, sunã tsõron wani yini wanda zukãta sunã bibbirkita a cikinsa, da gannai.
(38) Dõmin Allah Ya sãka musu da mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Ya ƙãra musu daga falalarsa. Kuma Allah Yanã azurta wanda Yake so, bã da lissafi ba.
(39) Kuma waɗanda suka ƙãfirta ayyukansu sunã kamar ƙawalwalniyã ga faƙo, mai ƙishirwa yanã zaton sa ruwa, har idan ya jẽ masa bai iske shi kõme ba, kuma ya sãmi Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisãbinsa. Kuma Allah Mai gaggãwar sakamako ne.
(40) Kõ kuwa kamar duffai a cikin tẽku mai zurfi, tãguwar ruwa tanã rufe da shi, daga bisansa akwai wata tãguwa, daga bisansa akwai wani girgije, duffai sãshensu a bisa sãshe, idan ya fitar da tãfinsa ba ya kusa ya gan shi. Kuma wanda Allah bai sanya masa haske ba, to, bã ya da wani haske.
(41) Shin, ba ka gani ba (cẽwa) lalle ne Allah, Wanda yake a cikin sammai da ƙasa sunã yi Masa tasbĩhi, kuma tsuntsaye sunã mãsu sanwa, kõwane lalle ya san sallarsa da tasbĩhinsa kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatãwa?
(42) Mulkin sammai da ƙasa ga Allah kawai yake, kuma zuwa ga Allah makõma take.
(43) Ashe, ba ka ganĩ ba, lalle ne Allah Yanã kõra girgije, sa'an nan kuma Ya haɗa a tsakãninsa sa'an nan kuma Ya sanya shi mai hauhawar jũna? Sai ka ga ruwa yanã fita daga tsattsakinsa, kuma Ya saukar daga waɗansu duwãtsu a cikinsa na ƙanƙarã daga sama, sai ya sãmu wanda Yake so da shi, kuma Ya karkatar da shi daga barin wanda Yake so. Hasken walƙiyarsa Yanã kusa ya tafi da gannai.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022