(55) Bãbu laifi a kansu game da ubanninsu, kuma bãbu game da ɗiyansu, kuma bãbu game da 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kuma bãbu game da mãtan mũminai, kuma bãbu game da abin da hannãyensu suka mallaka, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Yã kasance Mahalarci a kan kõme.
(56) Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.
(57) Lalle waɗanda ke cũtar Allah da MauzonSa Allah Yã la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma Yã yi musu tattalin azãba mai wulãkantarwa.
(58) Kuma waɗanda suke cũtar mũminai maza dã muminai mãtã, bã da wani abu da suka aikata ba to, lalle sun ɗauki ƙiren ƙarya da zunubi bayyananne.
(59) Yã kai Annabi! Ka ce wa mãtan aurenka da 'yã'yanka da mãtan mũminai su kusantar da ƙasã daga manyan tufãfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cũce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai Jin ƙai.
(60) Lalle, idan munãfukai da waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukãtansu, da mãsu tsẽgumi a cikin Madĩna, ba su hanu ba (daga hãlãyensu), lalle, zã Mu shũshũta ka a gare su, sa'an nan bã zã su yi maƙwabtaka da kai ba, a cikinta, fãce kaɗan.
(61) Sunã la'anannu, inda duka aka sãme su a kãmã su, kuma a karkashe su karkashẽwa.
(62) A kan hanyar Allah (ta gyaran jama'a) a cikin waɗanda suka shũɗe gabãninka, kuma bã zã ka sãmi musanyãwa ba ga hanyar Allah.