ص   سورة  : Saad


سورة Sura   ص   Saad
وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاءَ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا بَاطِلًا ۚ ذَٰلِكَ ظَنُّ الَّذِينَ كَفَرُوا ۚ فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا مِنَ النَّارِ (27) أَمْ نَجْعَلُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ كَالْمُفْسِدِينَ فِي الْأَرْضِ أَمْ نَجْعَلُ الْمُتَّقِينَ كَالْفُجَّارِ (28) كِتَابٌ أَنزَلْنَاهُ إِلَيْكَ مُبَارَكٌ لِّيَدَّبَّرُوا آيَاتِهِ وَلِيَتَذَكَّرَ أُولُو الْأَلْبَابِ (29) وَوَهَبْنَا لِدَاوُودَ سُلَيْمَانَ ۚ نِعْمَ الْعَبْدُ ۖ إِنَّهُ أَوَّابٌ (30) إِذْ عُرِضَ عَلَيْهِ بِالْعَشِيِّ الصَّافِنَاتُ الْجِيَادُ (31) فَقَالَ إِنِّي أَحْبَبْتُ حُبَّ الْخَيْرِ عَن ذِكْرِ رَبِّي حَتَّىٰ تَوَارَتْ بِالْحِجَابِ (32) رُدُّوهَا عَلَيَّ ۖ فَطَفِقَ مَسْحًا بِالسُّوقِ وَالْأَعْنَاقِ (33) وَلَقَدْ فَتَنَّا سُلَيْمَانَ وَأَلْقَيْنَا عَلَىٰ كُرْسِيِّهِ جَسَدًا ثُمَّ أَنَابَ (34) قَالَ رَبِّ اغْفِرْ لِي وَهَبْ لِي مُلْكًا لَّا يَنبَغِي لِأَحَدٍ مِّن بَعْدِي ۖ إِنَّكَ أَنتَ الْوَهَّابُ (35) فَسَخَّرْنَا لَهُ الرِّيحَ تَجْرِي بِأَمْرِهِ رُخَاءً حَيْثُ أَصَابَ (36) وَالشَّيَاطِينَ كُلَّ بَنَّاءٍ وَغَوَّاصٍ (37) وَآخَرِينَ مُقَرَّنِينَ فِي الْأَصْفَادِ (38) هَٰذَا عَطَاؤُنَا فَامْنُنْ أَوْ أَمْسِكْ بِغَيْرِ حِسَابٍ (39) وَإِنَّ لَهُ عِندَنَا لَزُلْفَىٰ وَحُسْنَ مَآبٍ (40) وَاذْكُرْ عَبْدَنَا أَيُّوبَ إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ أَنِّي مَسَّنِيَ الشَّيْطَانُ بِنُصْبٍ وَعَذَابٍ (41) ارْكُضْ بِرِجْلِكَ ۖ هَٰذَا مُغْتَسَلٌ بَارِدٌ وَشَرَابٌ (42)
الصفحة Page 455
(27) Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã.
(28) Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fãjirai makarkata?
(29) (Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni.
(30) Kuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi (Sulaimãn) mai mayar da al'amari ne ga Allah.
(31) A lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, a lõkacin maraice.
(32) Sai ya ce: "Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har (rãnã) ta faku da shãmaki!"
(33) "Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu.
(34) Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu.
(35) Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna. Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta.
(36) Sabõda haka Muka hõre masa iska tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa.
(37) Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna.)
(38) Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa.
(39) Wannan kyautarMu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike.
(40) Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurinMu da kyaun makõma.
(41) Kuma ka ambaci bãwanMu Ayyũba a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba."
(42) Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022