(112) Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa."
(113) "Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa."
(114) "Ban zama mai kõre mũminai ba."
(115) "Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa."
(116) Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa"
(117) Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni."
(118) "Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai."
(119) Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi.
(120) Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran.
(121) Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba.
(122) Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama.
(123) Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni.
(124) A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba?"
(125) "Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce."
(126) "Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
(127) "Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu."
(128) "Shin, kunã yin ginin sitadiyo a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa?"
(129) "Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama?"
(130) "Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa."
(131) "To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
(132) "Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani."
(133) "Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya."
(134) "Da gõnaki da marẽmari."
(135) "Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma."
(136) Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba."