(77) Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa.
(78) Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe.
(79) Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu.
(80) Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
(81) Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai.
(82) Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu.
(83) Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake.
(84) A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya.
(85) A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?"
(86) "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?"
(87) "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?"
(88) Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri.
(89) Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne."
(90) Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya.
(91) Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba?
(92) "Me ya sãme ku, bã ku magana?"
(93) Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma.
(94) Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa.
(95) Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa,
(96) "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"
(97) Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm."
(98) Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci.
(99) Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni."
(100) "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne."
(101) Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.
(102) To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri."