المائدة   سورة  : Al-Maaida


سورة Sura   المائدة   Al-Maaida
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّمَا الْخَمْرُ وَالْمَيْسِرُ وَالْأَنصَابُ وَالْأَزْلَامُ رِجْسٌ مِّنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ فَاجْتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ (90) إِنَّمَا يُرِيدُ الشَّيْطَانُ أَن يُوقِعَ بَيْنَكُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ فِي الْخَمْرِ وَالْمَيْسِرِ وَيَصُدَّكُمْ عَن ذِكْرِ اللَّهِ وَعَنِ الصَّلَاةِ ۖ فَهَلْ أَنتُم مُّنتَهُونَ (91) وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَاحْذَرُوا ۚ فَإِن تَوَلَّيْتُمْ فَاعْلَمُوا أَنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ (92) لَيْسَ عَلَى الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ جُنَاحٌ فِيمَا طَعِمُوا إِذَا مَا اتَّقَوا وَّآمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ ثُمَّ اتَّقَوا وَّآمَنُوا ثُمَّ اتَّقَوا وَّأَحْسَنُوا ۗ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ (93) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَيَبْلُوَنَّكُمُ اللَّهُ بِشَيْءٍ مِّنَ الصَّيْدِ تَنَالُهُ أَيْدِيكُمْ وَرِمَاحُكُمْ لِيَعْلَمَ اللَّهُ مَن يَخَافُهُ بِالْغَيْبِ ۚ فَمَنِ اعْتَدَىٰ بَعْدَ ذَٰلِكَ فَلَهُ عَذَابٌ أَلِيمٌ (94) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَقْتُلُوا الصَّيْدَ وَأَنتُمْ حُرُمٌ ۚ وَمَن قَتَلَهُ مِنكُم مُّتَعَمِّدًا فَجَزَاءٌ مِّثْلُ مَا قَتَلَ مِنَ النَّعَمِ يَحْكُمُ بِهِ ذَوَا عَدْلٍ مِّنكُمْ هَدْيًا بَالِغَ الْكَعْبَةِ أَوْ كَفَّارَةٌ طَعَامُ مَسَاكِينَ أَوْ عَدْلُ ذَٰلِكَ صِيَامًا لِّيَذُوقَ وَبَالَ أَمْرِهِ ۗ عَفَا اللَّهُ عَمَّا سَلَفَ ۚ وَمَنْ عَادَ فَيَنتَقِمُ اللَّهُ مِنْهُ ۗ وَاللَّهُ عَزِيزٌ ذُو انتِقَامٍ (95)
الصفحة Page 123
(90) Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri'a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la'alla ku ci nasara.
(91) Abin sani kawaĩ Shaiɗan yanã nufin ya aukar da adãwa da ƙeta a tsakãninku, a cikin giya da cãca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga sallah. To, shin, ku mãsu hanuwa ne?
(92) Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗã'a ga Manzo, kuma ku kiyãye. To, idan kun jũya, to, ku sani abin da kawai yake kan ManzonMu, iyarwa bayyananniya.
(93) Bãbu laifi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, a cikin abin da suka ci, idan sun yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sa'an nan suka yi taƙawa kuma suka yi ĩmãni, sa'an nan kuma suka yi taƙawa kuma suka kyautata. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.
(94) Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne, Allah zai jarraba ku da wani abu, daga farauta, hannuwanku da mãsunku sunã sãmun sa dõmin Allah Ya san wanda yake tsoron Sa a fake. To, wanda ya yi ta'addi a bãyan wannan, to, yanã da azãba mai raɗaɗi.
(95) Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kashe farauta alhãli kunã mãsu harama. Kuma wanda ya kashe shi daga gare ku, yanã mai ganganci, sai sakamako misãlin abin da ya kashe, daga dabbõbin ni'ima, ma'abuta ãdalci biyu daga cikinku sunã yin hukunci da shi. Ya zama hadaya mai isa ga Ka'aba ko kuwa kaffãra da abincin miskĩnai ko kuwa a matsayinsa ya yi azumi dõmin ya ɗanɗani masifar al'amarinsa. Allah Yã yafe laifi daga abin da ya gabãta. Kuma wanda ya kõma, to, Allah zai yi azãbar rãmuwa daga gare shi, kuma Allah Mabuwãyi ne, ma'abũcin azabãr rãmuwa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022