التوبة   سورة  : At-Tawba


سورة Sura   التوبة   At-Tawba
يَحْلِفُونَ بِاللَّهِ لَكُمْ لِيُرْضُوكُمْ وَاللَّهُ وَرَسُولُهُ أَحَقُّ أَن يُرْضُوهُ إِن كَانُوا مُؤْمِنِينَ (62) أَلَمْ يَعْلَمُوا أَنَّهُ مَن يُحَادِدِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَأَنَّ لَهُ نَارَ جَهَنَّمَ خَالِدًا فِيهَا ۚ ذَٰلِكَ الْخِزْيُ الْعَظِيمُ (63) يَحْذَرُ الْمُنَافِقُونَ أَن تُنَزَّلَ عَلَيْهِمْ سُورَةٌ تُنَبِّئُهُم بِمَا فِي قُلُوبِهِمْ ۚ قُلِ اسْتَهْزِئُوا إِنَّ اللَّهَ مُخْرِجٌ مَّا تَحْذَرُونَ (64) وَلَئِن سَأَلْتَهُمْ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلْعَبُ ۚ قُلْ أَبِاللَّهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ (65) لَا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُم بَعْدَ إِيمَانِكُمْ ۚ إِن نَّعْفُ عَن طَائِفَةٍ مِّنكُمْ نُعَذِّبْ طَائِفَةً بِأَنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ (66) الْمُنَافِقُونَ وَالْمُنَافِقَاتُ بَعْضُهُم مِّن بَعْضٍ ۚ يَأْمُرُونَ بِالْمُنكَرِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمَعْرُوفِ وَيَقْبِضُونَ أَيْدِيَهُمْ ۚ نَسُوا اللَّهَ فَنَسِيَهُمْ ۗ إِنَّ الْمُنَافِقِينَ هُمُ الْفَاسِقُونَ (67) وَعَدَ اللَّهُ الْمُنَافِقِينَ وَالْمُنَافِقَاتِ وَالْكُفَّارَ نَارَ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا ۚ هِيَ حَسْبُهُمْ ۚ وَلَعَنَهُمُ اللَّهُ ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ مُّقِيمٌ (68)
الصفحة Page 197
(62) Sunã rantsuwa da Allah sabõda ku, dõmin su yardar da ku. Kuma Allah da ManzonSa ne mafi cancantar su yardar da Shi, idan sun kasance mũminai.
(63) Shin, ba su sani ba cẽwa "Lalle ne wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, haƙĩƙa Yanã da wutar Jahannama, Yanã madawwami a cikinta? Waccan ita ce wulãkantãwa babba!"
(64) Munãfukai sunã tsõron a saukar da wata sũra a kansu, wadda take bã su lãbãri ga abin da yake cikin zukãtansu. Ka ce: "Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai da abin da kuke tsõro."
(65) Kuma lalle ne, idan ka tambaye, su haƙĩƙa, sunã cẽwa, "Abin sani kawai, mun kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili?"
(66) "Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyanĩmãninku. Idan Mun yãfe laifi ga wata ƙungiya daga gare ku, zã Mu azabta wata ƙungiya sabõda, lalle, sun kasance mãsu laifi."
(67) Munãfukai maza da munãfukai mãtã, sãshensu daga sãshe, sunã umurni da abin ƙi kuma sunã hani daga alhẽri. Kuma sunã damƙẽwar hannayensu. Sun mance Allah, sai Ya mantã da su. Lalle ne munãfukai sũ ne fãsiƙai.
(68) Allah yã yi wa'adi ga munãfukai maza da munãfukai mãtã da kãfirai da wutar Jahannama, sunã madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu. Kuma Allah Yã la'ance su, kuma sunã da azãba zaunanniya.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022