الرعد   سورة  : Ar-Ra'd


سورة Sura   الرعد   Ar-Ra'd
وَيَقُولُ الَّذِينَ كَفَرُوا لَسْتَ مُرْسَلًا ۚ قُلْ كَفَىٰ بِاللَّهِ شَهِيدًا بَيْنِي وَبَيْنَكُمْ وَمَنْ عِندَهُ عِلْمُ الْكِتَابِ (43)
ابراهيم Ibrahim
الر ۚ كِتَابٌ أَنزَلْنَاهُ إِلَيْكَ لِتُخْرِجَ النَّاسَ مِنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ بِإِذْنِ رَبِّهِمْ إِلَىٰ صِرَاطِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ (1) اللَّهِ الَّذِي لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ وَوَيْلٌ لِّلْكَافِرِينَ مِنْ عَذَابٍ شَدِيدٍ (2) الَّذِينَ يَسْتَحِبُّونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا عَلَى الْآخِرَةِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ اللَّهِ وَيَبْغُونَهَا عِوَجًا ۚ أُولَٰئِكَ فِي ضَلَالٍ بَعِيدٍ (3) وَمَا أَرْسَلْنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا بِلِسَانِ قَوْمِهِ لِيُبَيِّنَ لَهُمْ ۖ فَيُضِلُّ اللَّهُ مَن يَشَاءُ وَيَهْدِي مَن يَشَاءُ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (4) وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مُوسَىٰ بِآيَاتِنَا أَنْ أَخْرِجْ قَوْمَكَ مِنَ الظُّلُمَاتِ إِلَى النُّورِ وَذَكِّرْهُم بِأَيَّامِ اللَّهِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّكُلِّ صَبَّارٍ شَكُورٍ (5)
الصفحة Page 255
(43) Kuma waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: "Ba a aiko ka ba." Ka ce, "Allah Yã isa zama shaida a tsakãnina da tsakãninku da wanda yake a wurinsa akwai ilmin Littãfi."
ابراهيم Ibrahim
(1) A. L̃.R. Littãfi ne mun saukar da shi zuwa gare ka dõmin ka fitar da mutãne daga duhunhuna zuwa ga haske, da iznin Ubangijinsu, zuwa ga tafarkin Mabuwãyi, Abin gõdẽwa.
(2) Allah wanda Yake Yanã da abin da ke cikin sammai da cikin ƙasa. Kuma bone yã tabbata ga kãfirai daga azãba mai tsanani.
(3) Waɗanda suka fi son rãyuwar dũniya fiye da ta Lãhira, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sunã nẽman ta karkace. Waɗancan na a cikin ɓata mai nĩsa.
(4) Kuma ba Mu aika wani Manzo ba fãce da harshen mutãnensa dõmin ya bayyanã musu. Sa'an nan Allah Ya ɓatar da wanda Yake so kuma Ya shiryar da wanda Yake so, Kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
(5) Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Mũsã game, da ãyõin Mu cẽwa, "Ka fitar da mutãnenkadaga duhu zuwa ga haske. Kuma ka tunar musu da kwãnukan (masĩfun) Allah." Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi dõmin dukan mai yawan haƙuri, mai gõdiya.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022