التوبة   سورة  : At-Tawba


سورة Sura   التوبة   At-Tawba
انفِرُوا خِفَافًا وَثِقَالًا وَجَاهِدُوا بِأَمْوَالِكُمْ وَأَنفُسِكُمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ (41) لَوْ كَانَ عَرَضًا قَرِيبًا وَسَفَرًا قَاصِدًا لَّاتَّبَعُوكَ وَلَٰكِن بَعُدَتْ عَلَيْهِمُ الشُّقَّةُ ۚ وَسَيَحْلِفُونَ بِاللَّهِ لَوِ اسْتَطَعْنَا لَخَرَجْنَا مَعَكُمْ يُهْلِكُونَ أَنفُسَهُمْ وَاللَّهُ يَعْلَمُ إِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ (42) عَفَا اللَّهُ عَنكَ لِمَ أَذِنتَ لَهُمْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكَ الَّذِينَ صَدَقُوا وَتَعْلَمَ الْكَاذِبِينَ (43) لَا يَسْتَأْذِنُكَ الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ أَن يُجَاهِدُوا بِأَمْوَالِهِمْ وَأَنفُسِهِمْ ۗ وَاللَّهُ عَلِيمٌ بِالْمُتَّقِينَ (44) إِنَّمَا يَسْتَأْذِنُكَ الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَارْتَابَتْ قُلُوبُهُمْ فَهُمْ فِي رَيْبِهِمْ يَتَرَدَّدُونَ (45) ۞ وَلَوْ أَرَادُوا الْخُرُوجَ لَأَعَدُّوا لَهُ عُدَّةً وَلَٰكِن كَرِهَ اللَّهُ انبِعَاثَهُمْ فَثَبَّطَهُمْ وَقِيلَ اقْعُدُوا مَعَ الْقَاعِدِينَ (46) لَوْ خَرَجُوا فِيكُم مَّا زَادُوكُمْ إِلَّا خَبَالًا وَلَأَوْضَعُوا خِلَالَكُمْ يَبْغُونَكُمُ الْفِتْنَةَ وَفِيكُمْ سَمَّاعُونَ لَهُمْ ۗ وَاللَّهُ عَلِيمٌ بِالظَّالِمِينَ (47)
الصفحة Page 194
(41) Ku fita da yãƙi kunã mãsu sauƙãƙan kãyã da mãsu nauyi, kuma ku yi jihãdi da dũkiyõyinku da kuma rãyukanku a cikin hanyar Allah. Wancan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani.
(42) Dã yã kasance wata siffar dũniya ce: makusanciya, da tafiya matsakaiciya, dã sun bĩ ka, kuma amma fagen yã yi musu nĩsa. Kuma zã su yi ta yin rantsuwa da Allah, "Dã mun sãmi dãma, dã mun tafi tare da ku." Sunã halakar da kansu (da rantsuwar ƙarya) ne, kuma Allah Yanã sanin lalle, haƙĩƙa, sumaƙaryata ne.'
(43) Allah Ya yãfe maka laifi. Dõmin me ka yi musu izinin zama? Sai waɗanda suka yi gaskiya ssun bayyana a gare ka, kuma ka san maƙaryata.
(44) Waɗanda suke yin ĩmãnida Allah da Rãnar Lãhira, bã zã su nẽmi izininka ga yin, jihãdida dũkiyõyinsu da rãyukansu ba. Kuma Allah ne Masani ga mãsu taƙawa.
(45) Abin sani kawai, waɗanda bã sa ĩmãni da Allah, da Rãnar Lãhira, kuma zukãtansu suka yi shakka, sũ ne ke nẽman izininka, sa'an nan a cikin shakkarsu sunã ta yin kai kãwo.
(46) Kuma dã sun yi nufin fita, dã sun yi wani tattali sabõda shi, kuma amma Allah Ya ƙi zãburarsu, sai Ya nauyayar da zamansu. Kuma aka ce ku zauna tãre da mãsu zama.
(47) Dã sun fita a cikinku bã zã su ƙãre ku da kõme ba fãce da ɓarna, kuma lalle dã sun yi gaggãwar sanya annamĩmanci a tsakãninku, sunã nẽma muku fitina. Kuma a cikinku akwai 'yan rahõto sabõda su. Kuma Allah ne Masani ga azzãlumai,
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022