(3) An haramta muku mũshe da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da mãƙararriya da jefaffiya da mai gangarõwa da sõkakkiya, da abin da mãsu dãgi suka ci, fãce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na cãca wannan fãsiƙanci ne, A yau waɗanda suka kãfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõroNa. A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bã yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
(4) Suna tambayar ka cewa mene ne aka halatta musu? Ka ce: "An halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi da abin da kuka sanar (farauta) daga mãsu yin mĩki, kunã mãsu sakinsu daga hannuwanku, kunã sanar da su daga abin da Allah Ya sanar da ku. To, ku ci daga abin da suka kama sabõda ku, kuma ku ambaci sunan Allah a kansa, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako da yawã ne.
(5) A yau an halatta muku abũbuwa mãsu dãɗi kuma abincin waɗanda aka bai wa Littãfi halal ne a gare ku, kuma abincinku halal ne a gare su, da mãtã mãsu kãmun kai daga muminai da mãtã 'yã'ya daga waɗanda aka bai wa Littãfi a gabãninku idan kun je musu da sadãkõkinsu, kuna mãsu yin aure, ba masu yin zina ba, kuma bã mãsu riƙon abõkai ba. Kuma wanda ya kãfirta da ĩmãni to, lalle ne aikinsa yã ɓãci, kuma shĩ, a cikin Lãhira, yanã daga mãsu hasãra.