الشورى   سورة  : Ash-Shura


سورة Sura   الشورى   Ash-Shura
فَاطِرُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ جَعَلَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا وَمِنَ الْأَنْعَامِ أَزْوَاجًا ۖ يَذْرَؤُكُمْ فِيهِ ۚ لَيْسَ كَمِثْلِهِ شَيْءٌ ۖ وَهُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ (11) لَهُ مَقَالِيدُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ وَيَقْدِرُ ۚ إِنَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ (12) ۞ شَرَعَ لَكُم مِّنَ الدِّينِ مَا وَصَّىٰ بِهِ نُوحًا وَالَّذِي أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ وَمَا وَصَّيْنَا بِهِ إِبْرَاهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَىٰ ۖ أَنْ أَقِيمُوا الدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُوا فِيهِ ۚ كَبُرَ عَلَى الْمُشْرِكِينَ مَا تَدْعُوهُمْ إِلَيْهِ ۚ اللَّهُ يَجْتَبِي إِلَيْهِ مَن يَشَاءُ وَيَهْدِي إِلَيْهِ مَن يُنِيبُ (13) وَمَا تَفَرَّقُوا إِلَّا مِن بَعْدِ مَا جَاءَهُمُ الْعِلْمُ بَغْيًا بَيْنَهُمْ ۚ وَلَوْلَا كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ إِلَىٰ أَجَلٍ مُّسَمًّى لَّقُضِيَ بَيْنَهُمْ ۚ وَإِنَّ الَّذِينَ أُورِثُوا الْكِتَابَ مِن بَعْدِهِمْ لَفِي شَكٍّ مِّنْهُ مُرِيبٍ (14) فَلِذَٰلِكَ فَادْعُ ۖ وَاسْتَقِمْ كَمَا أُمِرْتَ ۖ وَلَا تَتَّبِعْ أَهْوَاءَهُمْ ۖ وَقُلْ آمَنتُ بِمَا أَنزَلَ اللَّهُ مِن كِتَابٍ ۖ وَأُمِرْتُ لِأَعْدِلَ بَيْنَكُمُ ۖ اللَّهُ رَبُّنَا وَرَبُّكُمْ ۖ لَنَا أَعْمَالُنَا وَلَكُمْ أَعْمَالُكُمْ ۖ لَا حُجَّةَ بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمُ ۖ اللَّهُ يَجْمَعُ بَيْنَنَا ۖ وَإِلَيْهِ الْمَصِيرُ (15)
الصفحة Page 484
(11) (Shĩ ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasa, Ya sanya muku ma'aura daga jinsinku, kuma (Ya sanya) daga dabbõbi maza da mãtã, Yanã halitta ku a cikinsu, wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani.
(12) Shĩ ne da mabuɗan sammai da ƙasa Yanã shimfiɗa arziki ga wanda ya so kuma Yanã hukuntãwa. Lalle ne, Shĩ Masani ne ga dukan kõme.
(13) Ya shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. Abin da kuke kira zuwa gare shi, ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyarSa.
(14) Kuma ba su rarraba ba fãce bãyan da ilmi ya jẽ musu, dõmin zãlunci a tsakãninsu kuma bã dõmin wata kalma tã gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali ambatacce, dã an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gãdar wa Littafi daga bãyansu, haƙiƙa, sunã cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto.
(15) Sabõda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zũciyõyinsu, kumaka ce, "Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi, kuma an umurce ni da in yi ãdalci a tsakãninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nã gare mu, kuma ayyukanku nã gare ku, kuma bãbu wata hujja a tsakãninmu da tsakãninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makõma take."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022