الأنعام   سورة  : Al-An'aam


سورة Sura   الأنعام   Al-An'aam
بَلْ بَدَا لَهُم مَّا كَانُوا يُخْفُونَ مِن قَبْلُ ۖ وَلَوْ رُدُّوا لَعَادُوا لِمَا نُهُوا عَنْهُ وَإِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ (28) وَقَالُوا إِنْ هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا الدُّنْيَا وَمَا نَحْنُ بِمَبْعُوثِينَ (29) وَلَوْ تَرَىٰ إِذْ وُقِفُوا عَلَىٰ رَبِّهِمْ ۚ قَالَ أَلَيْسَ هَٰذَا بِالْحَقِّ ۚ قَالُوا بَلَىٰ وَرَبِّنَا ۚ قَالَ فَذُوقُوا الْعَذَابَ بِمَا كُنتُمْ تَكْفُرُونَ (30) قَدْ خَسِرَ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِلِقَاءِ اللَّهِ ۖ حَتَّىٰ إِذَا جَاءَتْهُمُ السَّاعَةُ بَغْتَةً قَالُوا يَا حَسْرَتَنَا عَلَىٰ مَا فَرَّطْنَا فِيهَا وَهُمْ يَحْمِلُونَ أَوْزَارَهُمْ عَلَىٰ ظُهُورِهِمْ ۚ أَلَا سَاءَ مَا يَزِرُونَ (31) وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلَّا لَعِبٌ وَلَهْوٌ ۖ وَلَلدَّارُ الْآخِرَةُ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ (32) قَدْ نَعْلَمُ إِنَّهُ لَيَحْزُنُكَ الَّذِي يَقُولُونَ ۖ فَإِنَّهُمْ لَا يُكَذِّبُونَكَ وَلَٰكِنَّ الظَّالِمِينَ بِآيَاتِ اللَّهِ يَجْحَدُونَ (33) وَلَقَدْ كُذِّبَتْ رُسُلٌ مِّن قَبْلِكَ فَصَبَرُوا عَلَىٰ مَا كُذِّبُوا وَأُوذُوا حَتَّىٰ أَتَاهُمْ نَصْرُنَا ۚ وَلَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَاتِ اللَّهِ ۚ وَلَقَدْ جَاءَكَ مِن نَّبَإِ الْمُرْسَلِينَ (34) وَإِن كَانَ كَبُرَ عَلَيْكَ إِعْرَاضُهُمْ فَإِنِ اسْتَطَعْتَ أَن تَبْتَغِيَ نَفَقًا فِي الْأَرْضِ أَوْ سُلَّمًا فِي السَّمَاءِ فَتَأْتِيَهُم بِآيَةٍ ۚ وَلَوْ شَاءَ اللَّهُ لَجَمَعَهُمْ عَلَى الْهُدَىٰ ۚ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ الْجَاهِلِينَ (35)
الصفحة Page 131
(28) Ã'aha, abin da suka kasance suna ɓõyẽwa, daga gabãni, ya bayyana a gare su. Kuma dã an mayar da su, lalle dã sun kõma ga abin da aka hana su daga barinsa. Kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne.
(29) Kuma suka ce: "Ba ta zama ba, fãce rayuwarmu ta duniya, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
(30) Kuma dã kana gani, a lõkacin da aka tsayar da su ga UbangiJinsu, Ya ce: "Ashe wannan bai zama gaskiya ba?" Suka ce: "Nã'am, muna rantsuwa da Ubangijinmu!" Ya ce: "To ku ɗanɗani azaba sabõda abin da kuka kasance kuna yi na kãfirci."
(31) Lalle ne waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasara, har idan Sa'a ta je musu kwatsam, sai su ce: "Yã nadãmarmu a kan abin da muka yi sakaci a cikinta!" Alhãli kuwa su suna ɗaukar kayansu masu nauyi a kan bayayyakinsu. To, abin da suke ɗauka yã mũnana.
(32) Kuma rãyuwar dũniya ba ta zama ba, fãce wãsa da shagala, kuma lalle ne, Lãhira ce mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa. Shin, ba za ku yi hankali ba?
(33) Lalle ne Muna sani cewa haƙĩƙa, abin da suke faɗa yana ɓãta maka rai. To, lalle ne su, bã su ƙaryata ka (a cikin zukatansu) kuma amma azzãlumai da ãyõyin Allah suke musu.
(34) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, an ƙaryata manzanni daga gabãninka, sai suka yi haƙuri a kan abin da aka ƙaryata su, kuma aka cũtar da su, har taimakonMu ya je musu, kuma babu mai musanyãwa ga kalmõmin Allah. Kuma lalle ne (abin da yake natsar da kai) ya zo maka daga lãbãrin (annabãwan) farko.
(35) Kuma idan yã kasance cewa finjirewarsu tã yi nauyi a gare ka, to, idan kana iyãwa, ka nemi wani ɓullõ a cikin ƙasa, kõ kuwa wani tsãni a cikin sama dõmin ka zo musu da wata ãyã, (sai ka yi). Kuma dã Allah Yã so haƙĩƙa dã Yãtãra su a kan shiriya. Sabõda haka, kada lalle ka kasance daga jãhilai.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022