الحديد   سورة  : Al-Hadid


سورة Sura   الحديد   Al-Hadid
إِنَّهُ لَقُرْآنٌ كَرِيمٌ (77) فِي كِتَابٍ مَّكْنُونٍ (78) لَّا يَمَسُّهُ إِلَّا الْمُطَهَّرُونَ (79) تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ (80) أَفَبِهَٰذَا الْحَدِيثِ أَنتُم مُّدْهِنُونَ (81) وَتَجْعَلُونَ رِزْقَكُمْ أَنَّكُمْ تُكَذِّبُونَ (82) فَلَوْلَا إِذَا بَلَغَتِ الْحُلْقُومَ (83) وَأَنتُمْ حِينَئِذٍ تَنظُرُونَ (84) وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنكُمْ وَلَٰكِن لَّا تُبْصِرُونَ (85) فَلَوْلَا إِن كُنتُمْ غَيْرَ مَدِينِينَ (86) تَرْجِعُونَهَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ (87) فَأَمَّا إِن كَانَ مِنَ الْمُقَرَّبِينَ (88) فَرَوْحٌ وَرَيْحَانٌ وَجَنَّتُ نَعِيمٍ (89) وَأَمَّا إِن كَانَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِ (90) فَسَلَامٌ لَّكَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِ (91) وَأَمَّا إِن كَانَ مِنَ الْمُكَذِّبِينَ الضَّالِّينَ (92) فَنُزُلٌ مِّنْ حَمِيمٍ (93) وَتَصْلِيَةُ جَحِيمٍ (94) إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ الْيَقِينِ (95) فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ (96)
الحديد Al-Hadid
سَبَّحَ لِلَّهِ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (1) لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ (2) هُوَ الْأَوَّلُ وَالْآخِرُ وَالظَّاهِرُ وَالْبَاطِنُ ۖ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ (3)
الصفحة Page 537
(77) Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
(78) A cikin wani littafi tsararre.
(79) Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
(80) Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
(81) Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
(82) Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
(83) To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
(84) Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
(85) Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
(86) To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
(87) Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.
(88) To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
(89) Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
(90) Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
(91) Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
(92) Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
(93) Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
(94) Da ƙõnuwa da Jahĩm,
(95) Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
(96) Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.
الحديد Al-Hadid
(1) Abin da ke cikin sammai da ƙasa yã yi tasbĩhi ga Allah. Kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
(2) Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa: Yanã rãyarwa kuma Yanã kashẽwa, kuma Shĩ Mai ikon yi ne a kan kõme.
(3) Shĩ ne Na farko, Na ƙarshe, Bayyananne, Bõyayye, kuma Shĩ Masani ne ga dukkan kõme.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022