الجاثية   سورة  : Al-Jaathiya


سورة Sura   الجاثية   Al-Jaathiya
أَفَرَأَيْتَ مَنِ اتَّخَذَ إِلَٰهَهُ هَوَاهُ وَأَضَلَّهُ اللَّهُ عَلَىٰ عِلْمٍ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمْعِهِ وَقَلْبِهِ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِ غِشَاوَةً فَمَن يَهْدِيهِ مِن بَعْدِ اللَّهِ ۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ (23) وَقَالُوا مَا هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا الدُّنْيَا نَمُوتُ وَنَحْيَا وَمَا يُهْلِكُنَا إِلَّا الدَّهْرُ ۚ وَمَا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِنْ هُمْ إِلَّا يَظُنُّونَ (24) وَإِذَا تُتْلَىٰ عَلَيْهِمْ آيَاتُنَا بَيِّنَاتٍ مَّا كَانَ حُجَّتَهُمْ إِلَّا أَن قَالُوا ائْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ (25) قُلِ اللَّهُ يُحْيِيكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يَجْمَعُكُمْ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ لَا رَيْبَ فِيهِ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ (26) وَلِلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَيَوْمَ تَقُومُ السَّاعَةُ يَوْمَئِذٍ يَخْسَرُ الْمُبْطِلُونَ (27) وَتَرَىٰ كُلَّ أُمَّةٍ جَاثِيَةً ۚ كُلُّ أُمَّةٍ تُدْعَىٰ إِلَىٰ كِتَابِهَا الْيَوْمَ تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (28) هَٰذَا كِتَابُنَا يَنطِقُ عَلَيْكُم بِالْحَقِّ ۚ إِنَّا كُنَّا نَسْتَنسِخُ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (29) فَأَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَيُدْخِلُهُمْ رَبُّهُمْ فِي رَحْمَتِهِ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْمُبِينُ (30) وَأَمَّا الَّذِينَ كَفَرُوا أَفَلَمْ تَكُنْ آيَاتِي تُتْلَىٰ عَلَيْكُمْ فَاسْتَكْبَرْتُمْ وَكُنتُمْ قَوْمًا مُّجْرِمِينَ (31) وَإِذَا قِيلَ إِنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ وَالسَّاعَةُ لَا رَيْبَ فِيهَا قُلْتُم مَّا نَدْرِي مَا السَّاعَةُ إِن نَّظُنُّ إِلَّا ظَنًّا وَمَا نَحْنُ بِمُسْتَيْقِنِينَ (32)
الصفحة Page 501
(23) Shin, kã ga wanda ya riƙi son zũciyarsa sĩh ne abin bautawarsa, kuma Allah Ya ɓatar da shi a kan wani ilmi, Kuma Ya sa hatini a kan jinsa, da zũciyarsa, kuma Ya sa wata yãnã ã kan ganinsa? To, wãne ne zai shiryar da shi bãyan Allah? Shin to, bã zã ku yi tunãni ba?
(24) Kuma suka ce: "Bãbu kõme fãce rãyuwarmu ta dũniya; munã mutuwa kuma munã rãyuwa (da haihuwa) kuma bãbu abin da ke halaka mu sai zãmani." Alhãli kuwa (ko da suke faɗar maganar) bã su da wani ilmi game da wannan, bã su bin kõme face zato.
(25) Kuma idan anã karanta ãyõyinMu bayyanannu a kansu, bãbu abin da ya kasance hujjarsu fãce suka ce: "Ku zo mana da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."
(26) Ka ce: "Allah ne ke rãyar da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."
(27) "Kuma mulkin sammai da ƙasa na Allah ne, Shĩ kaɗai. Kuma rãnar da Sa'a ke tsayuwa, a rãnar nan mãsu ɓãtãwã (ga hujjõjin Allah dõmin su ki bin sharĩ'arSa) zã su yi hasãra."
(28) Kuma zã ka ga kõwace al'umma tanã gurfãne, kõwace al'umma anã kiran ta zuwa ga littãfinta. (A ce musu) "A yau anã sãka muku da abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
(29) "Wannan littãfinMu ne yanã yin magana a kanku da gas, kiya. Lalle Mũ, Mun kasanceMuna sauya rubũtun tamkar abin dakuka kasance kunã aikãtãwa."
(30) To, amma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, to, Ubangijinsu zai sanya su a cikin rahamarsa. Wannan shĩ ne babban rabo bayyananne.
(31) Kuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): "Shin, ãyõyĩNã ba su kasance anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu laifi?"
(32) "Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto (game da ita) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba."'
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022