الأنعام   سورة  : Al-An'aam


سورة Sura   الأنعام   Al-An'aam
وَلَا تَقْرَبُوا مَالَ الْيَتِيمِ إِلَّا بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ حَتَّىٰ يَبْلُغَ أَشُدَّهُ ۖ وَأَوْفُوا الْكَيْلَ وَالْمِيزَانَ بِالْقِسْطِ ۖ لَا نُكَلِّفُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا ۖ وَإِذَا قُلْتُمْ فَاعْدِلُوا وَلَوْ كَانَ ذَا قُرْبَىٰ ۖ وَبِعَهْدِ اللَّهِ أَوْفُوا ۚ ذَٰلِكُمْ وَصَّاكُم بِهِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ (152) وَأَنَّ هَٰذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمًا فَاتَّبِعُوهُ ۖ وَلَا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَن سَبِيلِهِ ۚ ذَٰلِكُمْ وَصَّاكُم بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ (153) ثُمَّ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ تَمَامًا عَلَى الَّذِي أَحْسَنَ وَتَفْصِيلًا لِّكُلِّ شَيْءٍ وَهُدًى وَرَحْمَةً لَّعَلَّهُم بِلِقَاءِ رَبِّهِمْ يُؤْمِنُونَ (154) وَهَٰذَا كِتَابٌ أَنزَلْنَاهُ مُبَارَكٌ فَاتَّبِعُوهُ وَاتَّقُوا لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ (155) أَن تَقُولُوا إِنَّمَا أُنزِلَ الْكِتَابُ عَلَىٰ طَائِفَتَيْنِ مِن قَبْلِنَا وَإِن كُنَّا عَن دِرَاسَتِهِمْ لَغَافِلِينَ (156) أَوْ تَقُولُوا لَوْ أَنَّا أُنزِلَ عَلَيْنَا الْكِتَابُ لَكُنَّا أَهْدَىٰ مِنْهُمْ ۚ فَقَدْ جَاءَكُم بَيِّنَةٌ مِّن رَّبِّكُمْ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ ۚ فَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن كَذَّبَ بِآيَاتِ اللَّهِ وَصَدَفَ عَنْهَا ۗ سَنَجْزِي الَّذِينَ يَصْدِفُونَ عَنْ آيَاتِنَا سُوءَ الْعَذَابِ بِمَا كَانُوا يَصْدِفُونَ (157)
الصفحة Page 149
(152) Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa. Kuma ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, bã Mu kallafã wa rai fãce iyãwarsa. Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi: Tsammãninku, kunã tunãwa.
(153) Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarrabu da ku daga barin hanyãTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi tsammãninku, kunã yin taƙawa.
(154) Sa'an nan kuma Mun bai wa Mũsã Littãfi, yanã cikakke bisa ga wanda ya kyautata (hukuncin Allah) da rarrabẽwa, daki-daki, ga kõwane abu, da shiriya da rahama, tsammãninsu, sunã yin ĩmãni da haɗuwa da Ubangijinsu.
(155) Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, sai ku bĩ shi kuma ku yi taƙawa, tsammãninku, anã jin ƙanku.
(156) (Dõmin) kada ku ce: "Abin sani kawai, an saukar da littãfi a kan ƙungiya biyu daga gabãninmu, kuma lalle ne mũ, mun kasance, daga karatunsu, haƙĩƙa, gãfilai."
(157) Kõ kuwa ku ce: "Dã dai lalle mũ an saukar da Littãfi a kanmu, haƙĩƙa, dã mun kasance mafiya, shiryuwa daga gare su." To, lalle ne wata hujja bayyananniya, daga Ubangijinku, tã zo muku, da shiriya da rahama. To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma ya finjire daga barinsu? Zã Mu sãka wa waɗanda suke finjirẽwa daga barin ãyõyinMu da mugunyar azãba, sabõda abin da suka kasance sunã yi na hinjirẽwa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022