الأنفال   سورة  : Al-Anfaal


سورة Sura   الأنفال   Al-Anfaal
فَلَمْ تَقْتُلُوهُمْ وَلَٰكِنَّ اللَّهَ قَتَلَهُمْ ۚ وَمَا رَمَيْتَ إِذْ رَمَيْتَ وَلَٰكِنَّ اللَّهَ رَمَىٰ ۚ وَلِيُبْلِيَ الْمُؤْمِنِينَ مِنْهُ بَلَاءً حَسَنًا ۚ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ (17) ذَٰلِكُمْ وَأَنَّ اللَّهَ مُوهِنُ كَيْدِ الْكَافِرِينَ (18) إِن تَسْتَفْتِحُوا فَقَدْ جَاءَكُمُ الْفَتْحُ ۖ وَإِن تَنتَهُوا فَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ وَإِن تَعُودُوا نَعُدْ وَلَن تُغْنِيَ عَنكُمْ فِئَتُكُمْ شَيْئًا وَلَوْ كَثُرَتْ وَأَنَّ اللَّهَ مَعَ الْمُؤْمِنِينَ (19) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَطِيعُوا اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَلَا تَوَلَّوْا عَنْهُ وَأَنتُمْ تَسْمَعُونَ (20) وَلَا تَكُونُوا كَالَّذِينَ قَالُوا سَمِعْنَا وَهُمْ لَا يَسْمَعُونَ (21) ۞ إِنَّ شَرَّ الدَّوَابِّ عِندَ اللَّهِ الصُّمُّ الْبُكْمُ الَّذِينَ لَا يَعْقِلُونَ (22) وَلَوْ عَلِمَ اللَّهُ فِيهِمْ خَيْرًا لَّأَسْمَعَهُمْ ۖ وَلَوْ أَسْمَعَهُمْ لَتَوَلَّوا وَّهُم مُّعْرِضُونَ (23) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اسْتَجِيبُوا لِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ إِذَا دَعَاكُمْ لِمَا يُحْيِيكُمْ ۖ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ يَحُولُ بَيْنَ الْمَرْءِ وَقَلْبِهِ وَأَنَّهُ إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ (24) وَاتَّقُوا فِتْنَةً لَّا تُصِيبَنَّ الَّذِينَ ظَلَمُوا مِنكُمْ خَاصَّةً ۖ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ (25)
الصفحة Page 179
(17) To, bã kũ ne kuka kashe su ba; kuma amma Allah ne Ya kashe su: kuma ba ka yi jĩfa ba a lõkacin da ka yi jĩfa; kuma amma Allah ne Ya yi jĩfar. Kuma dõminYa jarraba Musulmi da jarrabãwa mai kyau daga gare shi. Kuma Allah Mai ji ne, Masani.
(18) Wancan ne, kuma lalle ne, Allah Mai raunana kaidin kãfirai ne.
(19) Idan kun yi alfãnun cin nasara to lalle nasarar tã je muku, kuma idan kun hanu, to Shi ne Mafi alhẽri a gare ku, kuma idan kun kõma zã Mu kõma, kuma jama'arku bã zã ta wadãtar muku da kõme ba, kõ dã tã yi yawa. Kuma lalle ne cẽwa Allah Yanã tãre da mũminai!
(20) Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku jũya daga barinSa, alhãli kunã ji.
(21) Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka ce: "Mun ji, alhãli kuwa sũ bã su ji."
(22) Lalle ne, mafi sharrin dabbõbi a wurin Allah, sũ ne kurãme, bẽbãye, waɗanda bã, su yin hankali.
(23) Dã Allah Yã san wani alhẽri a cikinsu, dã Yã jiyar da su, kuma kõ da Yãjiyar da su, haƙĩƙa, dã sun jũya, alhãli sũ, sunã mãsu hinjirẽwa.
(24) Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku karɓa wa Allah, kuma ku karɓa wa Manzo, idan Ya kirãye ku zuwa ga abin da Yake rãyar da ku; Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã shãmakacẽwa a tsakãnin mutum da zũciyarsa, kuma lalle ne Shĩ, a zuwa gare Shi ake tãra ku.
(25) Kuma ku ji tsõron fitina wadda bã ta sãmun waɗanda suka yi zãlunci daga gare ku kẽɓe, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022