(47) Zuwa gare Shi ake mayar da sanin Sa'a. Kuma waɗansu 'yã'yan itãce bã su fita daga kwasfõfinsu, kuma wata mace bã ta yin ciki, kuma bã ta haihuwa, fãce da saninSa, kuma a rãnar da Yake kiran su (Ya ce): "Inã abõkan tãrayyaTa?" Sai su ce, "Mun sanar da Kai bãbu mai bãyar da shaida da haka nan daga gare mu."
(48) Kuma abin da suka kasance sunã kira a gabãnin haka ya ɓace musu, kuma suka yi zaton cẽwa bã su da wata mafakã.
(49) Mutum bã ya kõsãwa daga addu 'ar nẽman alhẽri kuma idan sharri ya shãfe shi, sai ya zama mai yanke kauna, Mai nũna kãsãwa.
(50) Kuma lalle idan Mun ɗanɗana masa wata rahama daga gareMu, daga bãyan wata cũta ta shãfe shi, lalle zai ce, "Wannan (ni'ima) tãwa ce kuma bã ni zaton Sã'a mai tsayuwa ce, kuma lalle idan aka mayar da ni zuwa ga Ubangijĩna, haƙĩƙa, inã da makõma mafi kyau, a wurinSa." To, lalle zã Mu bã da lãbãri ga waɗanda suka kãfirta game da abin da suka aikata, kuma lalle Munã ɗanɗana musu daga azãba, Mai kauri.
(51) Kuma idan Muka yi ni'ima ga mutum, sai ya bijire, kuma ya nĩsantar da gẽfensa, kuma idan sharri ya sãme shi, sai ya zama ma'abũcin addu'a mai fãɗi.
(52) Ka ce: "Ashe, kun gani! Idan (Alƙur'ãni) ya kasance daga Allah ne, sa'an nan kun kãfirta a game da Shi, wãne ne mafi ɓata daga wanda yake yanã a cikin sãɓani manisanci (daga gaskiya)?"
(53) Zã Mu nũna musu ãyõyinMu a cikin sãsanni da kuma cikin rãyukansu, har ya bayyana a gare su cẽwã lalle (Alƙur'ãni), shi ne gaskiya. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa ba, ga cẽwa lalle Shĩ halartacce ne a kan kowane abu ne?
(54) To lalle sũ, sunã a cikin shakka daga gamuwa da Ubangijinsu. To, lalle Shĩ, Mai kẽwayẽwane ga dukan kõme ne.