(27) Sa'an nan a Rãnar ¡iyãma (Allah) Yanã kunyatã su, kuma Yanã cẽwa: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã gãbã a cikin ɗaukaka sha'aninsu?" Waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulãkanci a yau da cũta sun tabbata a kan kãfirai."
(28) Waɗanda malãiku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu zãluntar kansu. Sai suka jẽfa nẽman sulhu (suka ce) "Ba mu kasance muna aikata wani mummũnan aiki ba." Kayya! Lalle Allah ne Masani ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
(29) Sai ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kunã madawwama a cikinta. Sa'an nan tir da mazaunin mãsu girman kai.
(30) Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce, "Alhẽri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lãhira ce mafi alhẽri." Kuma haƙĩƙa, mãdalla da gidan mãsu taƙawa.
(31) Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã da abin da suke so a cikinsu. Kamar haka Allah ke sãkã wa mãsu taƙawa.
(32) Waɗanda malã'iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã'ikun sunã cẽwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
(33) Shin sunã jiran wani abu? Fãce malã'iku su jẽ musu kõ kuwa umurnin Ubangijinka. Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zãlunce su ba, kuma amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
(34) Sai mũnãnan abũbuwan da suka aikata ya sãme su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu.