غافر   سورة  : Ghafir


سورة Sura   غافر   Ghafir
وَتَرَى الْمَلَائِكَةَ حَافِّينَ مِنْ حَوْلِ الْعَرْشِ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ رَبِّهِمْ ۖ وَقُضِيَ بَيْنَهُم بِالْحَقِّ وَقِيلَ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ (75)
غافر Ghafir
حم (1) تَنزِيلُ الْكِتَابِ مِنَ اللَّهِ الْعَزِيزِ الْعَلِيمِ (2) غَافِرِ الذَّنبِ وَقَابِلِ التَّوْبِ شَدِيدِ الْعِقَابِ ذِي الطَّوْلِ ۖ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ إِلَيْهِ الْمَصِيرُ (3) مَا يُجَادِلُ فِي آيَاتِ اللَّهِ إِلَّا الَّذِينَ كَفَرُوا فَلَا يَغْرُرْكَ تَقَلُّبُهُمْ فِي الْبِلَادِ (4) كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَالْأَحْزَابُ مِن بَعْدِهِمْ ۖ وَهَمَّتْ كُلُّ أُمَّةٍ بِرَسُولِهِمْ لِيَأْخُذُوهُ ۖ وَجَادَلُوا بِالْبَاطِلِ لِيُدْحِضُوا بِهِ الْحَقَّ فَأَخَذْتُهُمْ ۖ فَكَيْفَ كَانَ عِقَابِ (5) وَكَذَٰلِكَ حَقَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ عَلَى الَّذِينَ كَفَرُوا أَنَّهُمْ أَصْحَابُ النَّارِ (6) الَّذِينَ يَحْمِلُونَ الْعَرْشَ وَمَنْ حَوْلَهُ يُسَبِّحُونَ بِحَمْدِ رَبِّهِمْ وَيُؤْمِنُونَ بِهِ وَيَسْتَغْفِرُونَ لِلَّذِينَ آمَنُوا رَبَّنَا وَسِعْتَ كُلَّ شَيْءٍ رَّحْمَةً وَعِلْمًا فَاغْفِرْ لِلَّذِينَ تَابُوا وَاتَّبَعُوا سَبِيلَكَ وَقِهِمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ (7)
الصفحة Page 467
(75) Kuma kanã ganin malã'iku sunã mãsu tsayãwa da haƙƙoƙin da aka ɗõra musu daga kẽwayen Al'arshi, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu. Kuma aka yi hukunci a tsakãninsu da gaskiya. Kuma aka ce, "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu."
غافر Ghafir
(1) Ḥ. M̃.
(2) Saukar da Littãfi daga Allah ne, Mabuwãyi, Masani.
(3) Mai gãfarta zunubi kuma Mai karɓar tũba Mai tsananin azãba, Mai wadãtarwa bãbu abin bautawa fãce Shi, zuwa gare Shi makõma take.
(4) Bãbu mai jãyayya a cikin ãyõyin Allah, fãce waɗanda suka kãfirta. Sabõda haka kada jũyãwarsu a cikin garũruwa ta rũɗe ka
(5) Mutãnen Nũhu sun ƙaryata a gabãninsu, da ƙungiyõyin da suke a bãyansu, kuma kõwace al'umma tã yi nufi game da Manzonsu, dõmin su kãmã shi. Kuma suka yi jãyayya da ƙarya dõmin su gusar da gaskiya da ita. Sai Na kãmã su. To, yãya azãbãTa take?
(6) Kuma kamar haka kalmar Ubangijinka ta wajaba a kan waɗanda suka kãfirta, dõmin sũ 'yan wutã ne.
(7) Waɗanda ke ɗaukar Al'arshi da waɗanda ke kẽwayenta, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, kuma sunã yin ĩmãni da Shi, kuma sunã yin istigfãri dõmin waɗanda suka yi ĩmãni, (sunã cẽwa), "Yã Ubangijinmu! Kã yalwaci dukan kõme da rahama da ilmi to Ka yi gãfara ga waɗanda suka tũba kuma suka bi hanyarKa, kuma Ka tsare musu azãbar Jahĩm."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022