الكهف   سورة  : Al-Kahf


سورة Sura   الكهف   Al-Kahf
وَلَقَدْ صَرَّفْنَا فِي هَٰذَا الْقُرْآنِ لِلنَّاسِ مِن كُلِّ مَثَلٍ ۚ وَكَانَ الْإِنسَانُ أَكْثَرَ شَيْءٍ جَدَلًا (54) وَمَا مَنَعَ النَّاسَ أَن يُؤْمِنُوا إِذْ جَاءَهُمُ الْهُدَىٰ وَيَسْتَغْفِرُوا رَبَّهُمْ إِلَّا أَن تَأْتِيَهُمْ سُنَّةُ الْأَوَّلِينَ أَوْ يَأْتِيَهُمُ الْعَذَابُ قُبُلًا (55) وَمَا نُرْسِلُ الْمُرْسَلِينَ إِلَّا مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ ۚ وَيُجَادِلُ الَّذِينَ كَفَرُوا بِالْبَاطِلِ لِيُدْحِضُوا بِهِ الْحَقَّ ۖ وَاتَّخَذُوا آيَاتِي وَمَا أُنذِرُوا هُزُوًا (56) وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّن ذُكِّرَ بِآيَاتِ رَبِّهِ فَأَعْرَضَ عَنْهَا وَنَسِيَ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ ۚ إِنَّا جَعَلْنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ أَكِنَّةً أَن يَفْقَهُوهُ وَفِي آذَانِهِمْ وَقْرًا ۖ وَإِن تَدْعُهُمْ إِلَى الْهُدَىٰ فَلَن يَهْتَدُوا إِذًا أَبَدًا (57) وَرَبُّكَ الْغَفُورُ ذُو الرَّحْمَةِ ۖ لَوْ يُؤَاخِذُهُم بِمَا كَسَبُوا لَعَجَّلَ لَهُمُ الْعَذَابَ ۚ بَل لَّهُم مَّوْعِدٌ لَّن يَجِدُوا مِن دُونِهِ مَوْئِلًا (58) وَتِلْكَ الْقُرَىٰ أَهْلَكْنَاهُمْ لَمَّا ظَلَمُوا وَجَعَلْنَا لِمَهْلِكِهِم مَّوْعِدًا (59) وَإِذْ قَالَ مُوسَىٰ لِفَتَاهُ لَا أَبْرَحُ حَتَّىٰ أَبْلُغَ مَجْمَعَ الْبَحْرَيْنِ أَوْ أَمْضِيَ حُقُبًا (60) فَلَمَّا بَلَغَا مَجْمَعَ بَيْنِهِمَا نَسِيَا حُوتَهُمَا فَاتَّخَذَ سَبِيلَهُ فِي الْبَحْرِ سَرَبًا (61)
الصفحة Page 300
(54) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun jujjũya, a cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane irin misãli ga mutãne (dõmin su gãne, su bi sharĩ'a), kuma mutum yã kasance mafi yawan abu ga jidãli.
(55) Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni a lõkacinda shiriya ta zo musu, kuma su nẽmi gãfara daga Ubangijinsu, fãce hanyar farko ta je musu kõ kuma azãba ta jẽ musu nau'i-nau'i.
(56) Kuma ba Mu aika Manzanni ba fãce sunã mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi, kuma waɗanda suka kãfirta sunã jidãli da ƙarya dõmin su ɓãta gaskiya da ita, kuma suka riƙi ãyõyiNa da abin da aka yi musu gargaɗi da shi abin izgili.
(57) Kuma wãne ne mafi zãlunci daga wanda aka tunãtar game da ãyõyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannãyensa suka gabãtar? Lalle ne Mũ, Mun sanya abũbuwan rufi a kan zukãtansu dõmin kada su fahimcẽ shi, kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi, kuma idan kã kĩrayẽ su zuwa ga shiriya, to, bã zã su shiryu ba, a sa'an nan, har abada.
(58) Kuma Ubangijinka Mai gãfara ne, Ma'abũcin rahama. Dã Yanã kãma su sabõda abin da suka sanã'anta, lalle ne, dã Ya gaggauta azãba a gare su. Ã'a, sunã da lõkacin alkawari, (wanda) bã zã su sãmi wata makõma ba, baicinSa.
(59) Kuma waɗancan alƙaryu Mun halaka su, a lõkacin da suka yi zãlunci, kuma Muka sanya lõkacin alkawarin, ga halaka su.
(60) Kuma a lõkacin da Mũsã ya ce wa yãronsa, "Bã zan gushe ba sai na isa mahaɗar tẽku biyu, kõ in shũɗe da tafiya shekara da shẽkaru."
(61) To, a lõkacin da suka isa mahaɗar tsakãninsu sai suka manta kĩfinsu, sai ya kãma tafarkinsa a cikin tẽku kamar bĩga.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022