القمر   سورة  : Al-Qamar


سورة Sura   القمر   Al-Qamar
وَمَا أَمْرُنَا إِلَّا وَاحِدَةٌ كَلَمْحٍ بِالْبَصَرِ (50) وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا أَشْيَاعَكُمْ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ (51) وَكُلُّ شَيْءٍ فَعَلُوهُ فِي الزُّبُرِ (52) وَكُلُّ صَغِيرٍ وَكَبِيرٍ مُّسْتَطَرٌ (53) إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَنَهَرٍ (54) فِي مَقْعَدِ صِدْقٍ عِندَ مَلِيكٍ مُّقْتَدِرٍ (55)
الرحمن Ar-Rahmaan
الرَّحْمَٰنُ (1) عَلَّمَ الْقُرْآنَ (2) خَلَقَ الْإِنسَانَ (3) عَلَّمَهُ الْبَيَانَ (4) الشَّمْسُ وَالْقَمَرُ بِحُسْبَانٍ (5) وَالنَّجْمُ وَالشَّجَرُ يَسْجُدَانِ (6) وَالسَّمَاءَ رَفَعَهَا وَوَضَعَ الْمِيزَانَ (7) أَلَّا تَطْغَوْا فِي الْمِيزَانِ (8) وَأَقِيمُوا الْوَزْنَ بِالْقِسْطِ وَلَا تُخْسِرُوا الْمِيزَانَ (9) وَالْأَرْضَ وَضَعَهَا لِلْأَنَامِ (10) فِيهَا فَاكِهَةٌ وَالنَّخْلُ ذَاتُ الْأَكْمَامِ (11) وَالْحَبُّ ذُو الْعَصْفِ وَالرَّيْحَانُ (12) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (13) خَلَقَ الْإِنسَانَ مِن صَلْصَالٍ كَالْفَخَّارِ (14) وَخَلَقَ الْجَانَّ مِن مَّارِجٍ مِّن نَّارٍ (15) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ (16)
الصفحة Page 531
(50) Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido.
(51) Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni?
(52) Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai.
(53) Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne.
(54) Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna.
(55) A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa.
الرحمن Ar-Rahmaan
(1) (Allah) Mai rahama.
(2) Yã sanar da Alƙur'ani.
(3) Yã halitta mutum.
(4) Yã sanar da shi bayãni (magana).
(5) Rãnã da watã a kan lissãfi suke.
(6) Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i.
(7) Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli.
(8) Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin.
(9) Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin.
(10) Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai.
(11) A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa.
(12) Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi.
(13) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku kuke ƙaryatãwa?
(14) Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko.
(15) Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã.
(16) To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa?
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022