الكافرون Al-Kaafiroon
(1) Ka ce: "Ya kũ kãfirai!"
(2) "Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba."
(3) "Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba."
(4) "Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba."
(5) "Kuma kũ, ba ku zama mãsu bautã wa abin da nake bautã wa ba."
(6) "Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni."
النصر An-Nasr
(1) Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara.
(2) Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, ƙungiya-ƙungiya.
(3) To, ka yi tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne.
المسد Al-Masad
(1) Hannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka.
(2) Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra.
(3) Zã ya shiga wuta mai hũruwa.
(4) Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta).
(5) A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma).