(57) "Ko kuma (kada) ya ce: 'Da Allah Ya shiryar da ni, dã na kasance daga mãsu taƙawa.'"
(58) "Ko kuma (kada (ya ce: a lõkacin da yake ganin azãba, 'Dã lalle a ce inã da wata kõmawa (zuwa dũniya) dõmin in kasance daga mãsu kyautatãwa.'"
(59) "Na'am! Lalle ne ãyõyiNa sun jẽ maka, sai ka ƙaryata a game da su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kãfirai."
(60) Kuma a Rãnar ¡iyãma kanã ganin waɗanda suka yi ƙarya ga Allah fuskõkinsu sunã mãsu yin baƙi. Ashe bãbu mazauni a cikin Jahannama ga mãsu girman kai?
(61) Kuma Allah na tsĩrar da waɗanda suka yi taƙawa a game da wurin sãmun babban rabonsu, cũta bã zã tashãfe su ba, kuma ba su zama sunã baƙin ciki ba.
(62) Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme.
(63) Shĩ ke da mabũɗan sammai da ƙasã. Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra.
(64) Ka ce: "Shin, wanin Allah kuke umurni na da in bauta wa? Yã ku jãhilai!"
(65) Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra."
(66) Ã'aha! Ka bauta wa Allah kaɗai, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya.
(67) Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi.