يوسف   سورة  : Yusuf


سورة Sura   يوسف   Yusuf
قَالَ يَا بُنَيَّ لَا تَقْصُصْ رُؤْيَاكَ عَلَىٰ إِخْوَتِكَ فَيَكِيدُوا لَكَ كَيْدًا ۖ إِنَّ الشَّيْطَانَ لِلْإِنسَانِ عَدُوٌّ مُّبِينٌ (5) وَكَذَٰلِكَ يَجْتَبِيكَ رَبُّكَ وَيُعَلِّمُكَ مِن تَأْوِيلِ الْأَحَادِيثِ وَيُتِمُّ نِعْمَتَهُ عَلَيْكَ وَعَلَىٰ آلِ يَعْقُوبَ كَمَا أَتَمَّهَا عَلَىٰ أَبَوَيْكَ مِن قَبْلُ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْحَاقَ ۚ إِنَّ رَبَّكَ عَلِيمٌ حَكِيمٌ (6) ۞ لَّقَدْ كَانَ فِي يُوسُفَ وَإِخْوَتِهِ آيَاتٌ لِّلسَّائِلِينَ (7) إِذْ قَالُوا لَيُوسُفُ وَأَخُوهُ أَحَبُّ إِلَىٰ أَبِينَا مِنَّا وَنَحْنُ عُصْبَةٌ إِنَّ أَبَانَا لَفِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ (8) اقْتُلُوا يُوسُفَ أَوِ اطْرَحُوهُ أَرْضًا يَخْلُ لَكُمْ وَجْهُ أَبِيكُمْ وَتَكُونُوا مِن بَعْدِهِ قَوْمًا صَالِحِينَ (9) قَالَ قَائِلٌ مِّنْهُمْ لَا تَقْتُلُوا يُوسُفَ وَأَلْقُوهُ فِي غَيَابَتِ الْجُبِّ يَلْتَقِطْهُ بَعْضُ السَّيَّارَةِ إِن كُنتُمْ فَاعِلِينَ (10) قَالُوا يَا أَبَانَا مَا لَكَ لَا تَأْمَنَّا عَلَىٰ يُوسُفَ وَإِنَّا لَهُ لَنَاصِحُونَ (11) أَرْسِلْهُ مَعَنَا غَدًا يَرْتَعْ وَيَلْعَبْ وَإِنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ (12) قَالَ إِنِّي لَيَحْزُنُنِي أَن تَذْهَبُوا بِهِ وَأَخَافُ أَن يَأْكُلَهُ الذِّئْبُ وَأَنتُمْ عَنْهُ غَافِلُونَ (13) قَالُوا لَئِنْ أَكَلَهُ الذِّئْبُ وَنَحْنُ عُصْبَةٌ إِنَّا إِذًا لَّخَاسِرُونَ (14)
الصفحة Page 236
(5) Ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Kada ka faɗi mafarkinka ga 'yan'uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaidan ga mutum, haƙĩƙa, maƙiyi ne bayyanãnne.
(6) "Kuma kãmar wancan ne, Ubangijinka Yake zãɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar lãbãrai, kuma ya cika ni'imõminSa a kanka, kuma a kan gidan Yãƙũba kãmar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabãni, Ibrãhĩm da Is'hãƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima."
(7) Lalle ne, haƙĩƙa, ãyõyi sun kasance ga Yũsufu da 'yan'uwansa dõmin mãsu tambaya.
(8) A lõkacin da suka ce: lalle ne Yũsufu da ɗan'uwansa ne mafiya sõyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhãli kuwa mũ jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙĩƙa, yanã cikin ɓata bayyananniya.
(9) Ku kashe Yũsufu, kõ kuwa ku jẽfa shi a wata ƙasa, fuskar ubanku ta wõfinta sabõda ku, kuma ku kasance a bãyansa mutãne sãlihai.
(10) Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Kada ku kashe Yũsufu. Ku jẽfa shi a cikin duhun rĩjiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance mãsu aikatãwa ne."
(11) Suka ce: "Yã bãbanmu! Mẽne ne a gare ka ba ka amince mana ba a kan Yũsufu, alhãlikuwa lalle ne mũ, haƙãƙa mãsu nashĩha muke a gare shi?"
(12) "Ka bar shi tãre da mu a gõbe, ya ji dãɗi, kuma ya yi wãsa. Kuma lalle ne mu, a gare shi, mãsu tsaro ne."
(13) Ya ce: "Lalle ne ni, haƙãƙa yanã ɓãta mini rai ku tafii da shi, Kuma inã tsõron kerkẽci ya cinye shi, alhãli ku kuwa kunã mãsu shagala daga gare shi."
(14) Suka ce: "Haƙĩƙa idan kerkẽci ya cinye shi, alhãli kuwa munã dangin jũna, lalle ne mũ, a sa'an nan, hakĩka, mun zama mãsu hasãra."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022