الأنفال   سورة  : Al-Anfaal


سورة Sura   الأنفال   Al-Anfaal
وَمَا لَهُمْ أَلَّا يُعَذِّبَهُمُ اللَّهُ وَهُمْ يَصُدُّونَ عَنِ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَمَا كَانُوا أَوْلِيَاءَهُ ۚ إِنْ أَوْلِيَاؤُهُ إِلَّا الْمُتَّقُونَ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ (34) وَمَا كَانَ صَلَاتُهُمْ عِندَ الْبَيْتِ إِلَّا مُكَاءً وَتَصْدِيَةً ۚ فَذُوقُوا الْعَذَابَ بِمَا كُنتُمْ تَكْفُرُونَ (35) إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا يُنفِقُونَ أَمْوَالَهُمْ لِيَصُدُّوا عَن سَبِيلِ اللَّهِ ۚ فَسَيُنفِقُونَهَا ثُمَّ تَكُونُ عَلَيْهِمْ حَسْرَةً ثُمَّ يُغْلَبُونَ ۗ وَالَّذِينَ كَفَرُوا إِلَىٰ جَهَنَّمَ يُحْشَرُونَ (36) لِيَمِيزَ اللَّهُ الْخَبِيثَ مِنَ الطَّيِّبِ وَيَجْعَلَ الْخَبِيثَ بَعْضَهُ عَلَىٰ بَعْضٍ فَيَرْكُمَهُ جَمِيعًا فَيَجْعَلَهُ فِي جَهَنَّمَ ۚ أُولَٰئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ (37) قُل لِّلَّذِينَ كَفَرُوا إِن يَنتَهُوا يُغْفَرْ لَهُم مَّا قَدْ سَلَفَ وَإِن يَعُودُوا فَقَدْ مَضَتْ سُنَّتُ الْأَوَّلِينَ (38) وَقَاتِلُوهُمْ حَتَّىٰ لَا تَكُونَ فِتْنَةٌ وَيَكُونَ الدِّينُ كُلُّهُ لِلَّهِ ۚ فَإِنِ انتَهَوْا فَإِنَّ اللَّهَ بِمَا يَعْمَلُونَ بَصِيرٌ (39) وَإِن تَوَلَّوْا فَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ مَوْلَاكُمْ ۚ نِعْمَ الْمَوْلَىٰ وَنِعْمَ النَّصِيرُ (40)
الصفحة Page 181
(34) Kuma mẽne ne a gare su da Allah ba zai yi musu azãba ba, alhãli kuwa sũ, sunã kangẽwa daga Masallaci Mai alfarma kuma ba su kasance majiɓintanSa ba? Bãbu majiɓintanSa fãce mãsu taƙawa. Kuma mafi yawansu ba su sani ba.
(35) Kuma sallarsu a wurin ¦ãkin ba ta kasance ba fãce shẽwa da yãyã; sai ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci.
(36) Lalle ne waɗanda suka kãfirta, sunã ciyar da dũkiyõyinsu, dõmin su kange daga hanyar Allah; to, zã a su ciyar da ita, sa' an nan kuma ta kasance nadãma a kansu, sa'an nan kuma a rinjãye su. Kuma waɗanda suka kãfirta zuwa ga Jahannama ake tãra su;
(37) Dõmin Allah Ya rarrabe mummũna daga mai kyau, kuma Ya sanya mummũnan, sãshensa a kan sãshe, sa'an nan Ya shirga shi gabã daya, sa'an nan Ya sanyã shi a cikin Jahannama. Waɗannan sũ ne mãsu hasãra.
(38) Ka ce wa waɗanda suka kãfirta, idan sun hanu, zã a gãfarta musu abin da ya riga ya shige, kuma idan sun kõma, to, hanyar kãfiran farko, haƙĩƙa, ta shũɗe.
(39) Kuma ku yãƙe su har wata fitina bã zã ta kasance ba, kuma addini dukansa ya kasance na Allah. To, idan sun hanu to lalle ne, Allah ia abin da kuke aikatãwa Mai gani ne.
(40) Kuma idan sun jũya, to, ku sani cẽwa lalle Allah ne Majiɓincinku: Mãdalla da Majiɓinci, kuma mãdalla da Mai taimako, Shĩ.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022