(39) Kuma ¡ãrũna da Fir'auna da Hãmãna, kuma lalle Mũsaya je musu da hujjõji, sai suka yi girman kai a cikin ƙasã kuma ba su kasance mãsu tsẽrẽwa ba.
(40) Sabõda haka kõwanensu Mun kama shi da laifinsa. Watau daga cikinsu akwai wanda Muka aika iskar tsakuwa a kansa kuma daga cikinsu akwai wanda tsãwa ta kãmã, kuma daga cikinsu akwai wanda Muka birkice ƙasã da shi kuma daga cikinsu akwai wanda Muka nutsar. Bã ya yiwuwa ga Allah Ya zãlunce su, amma sun kasance kansu suke zãlunta.
(41) Misãlin waɗanda suka riƙi waɗansu masõya waɗanda bã Allah ba, kamar misãlin gizõgizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhãli kuwa lalle mafi raunin gidãje, shĩ ne gidan gizogizo, dã sun kasance sunã sane.
(42) Lalle Allah Yanã sane da abin da suke kira wanda bã Shi ba na wani abu duka kuma shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima.
(43) Kuma waɗancan misãlan Munã bayyana su ga mutãne kuma bãbu mai hankalta da su sai mãsu ilmi.
(44) Allah Ya halitta sammai da ƙasa da gaskiya. Lalle cikin wancan akwai ãyã ga mũminai.
(45) Ka karanta abin da ake yin wahayi zuwa gare ka daga Littãfi, kuma ka tsayar da salla. Lalle salla tanã hanãwa daga alfãsha da abni ƙyãma, kuma lalle ambaton Allah ya fi girma, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke aikatãwa.