يوسف   سورة  : Yusuf


سورة Sura   يوسف   Yusuf
وَمَا تَسْأَلُهُمْ عَلَيْهِ مِنْ أَجْرٍ ۚ إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ (104) وَكَأَيِّن مِّنْ آيَةٍ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ يَمُرُّونَ عَلَيْهَا وَهُمْ عَنْهَا مُعْرِضُونَ (105) وَمَا يُؤْمِنُ أَكْثَرُهُم بِاللَّهِ إِلَّا وَهُم مُّشْرِكُونَ (106) أَفَأَمِنُوا أَن تَأْتِيَهُمْ غَاشِيَةٌ مِّنْ عَذَابِ اللَّهِ أَوْ تَأْتِيَهُمُ السَّاعَةُ بَغْتَةً وَهُمْ لَا يَشْعُرُونَ (107) قُلْ هَٰذِهِ سَبِيلِي أَدْعُو إِلَى اللَّهِ ۚ عَلَىٰ بَصِيرَةٍ أَنَا وَمَنِ اتَّبَعَنِي ۖ وَسُبْحَانَ اللَّهِ وَمَا أَنَا مِنَ الْمُشْرِكِينَ (108) وَمَا أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ إِلَّا رِجَالًا نُّوحِي إِلَيْهِم مِّنْ أَهْلِ الْقُرَىٰ ۗ أَفَلَمْ يَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَيَنظُرُوا كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۗ وَلَدَارُ الْآخِرَةِ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ اتَّقَوْا ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ (109) حَتَّىٰ إِذَا اسْتَيْأَسَ الرُّسُلُ وَظَنُّوا أَنَّهُمْ قَدْ كُذِبُوا جَاءَهُمْ نَصْرُنَا فَنُجِّيَ مَن نَّشَاءُ ۖ وَلَا يُرَدُّ بَأْسُنَا عَنِ الْقَوْمِ الْمُجْرِمِينَ (110) لَقَدْ كَانَ فِي قَصَصِهِمْ عِبْرَةٌ لِّأُولِي الْأَلْبَابِ ۗ مَا كَانَ حَدِيثًا يُفْتَرَىٰ وَلَٰكِن تَصْدِيقَ الَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ وَتَفْصِيلَ كُلِّ شَيْءٍ وَهُدًى وَرَحْمَةً لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ (111)
الصفحة Page 248
(104) Kuma bã ka tambayar su wata lãdã a kansa. Shĩ bai zama ba fãce ambato dõmin halittu.
(105) Kuma da yawa, wata ãyã a cikin sammai da ƙasa sunã shũɗẽwa a kanta kuma sũ, sunã bijirẽwa daga gare ta.
(106) Kuma mafi yawansu ba su yin ĩmãni da Allah fãce kuma sunã mãsu shirki.
(107) Shin fa, sun amince cẽwa wata masĩfa daga azãbar Allah ta zo musu ko kuwa Tãshin ¡iyãma ta zo musu kwatsam, alhãli sũ ba su sani ba?
(108) Ka ce: "Wannan ce hanyãta; inã kira zuwa ga Allah a kan basĩra, nĩ da waɗanda suka bĩ ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Nĩ kuma, ban zama daga mãsu shirki ba."
(109) Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã wahayi zuwa gare su, daga mutãnen ƙauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, dõmin su dũbayadda ãƙibar waɗanda suka kasance daga gabãninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lãhira shĩ ne mafi alhẽri ga waɗanda suka yi taƙawa? Shin fa, bã ku hankalta?
(110) Har a lõkacin da Manzanni suka yanke tsammãni, kuma suka yi zaton cẽwa an jingina suga ƙarya, sai taimakonMu ya je masu, Sa'an nan Mu tsẽrar da wanda Muke so, kuma bã a mayar da azãbarMu daga mutãne mãsu laifi.
(111) Lalle ne haƙĩƙa abin kula yã kasance a cikin ƙissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabẽwar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suka yi ĩmãni.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022