الروم   سورة  : Ar-Room


سورة Sura   الروم   Ar-Room
وَإِذَا مَسَّ النَّاسَ ضُرٌّ دَعَوْا رَبَّهُم مُّنِيبِينَ إِلَيْهِ ثُمَّ إِذَا أَذَاقَهُم مِّنْهُ رَحْمَةً إِذَا فَرِيقٌ مِّنْهُم بِرَبِّهِمْ يُشْرِكُونَ (33) لِيَكْفُرُوا بِمَا آتَيْنَاهُمْ ۚ فَتَمَتَّعُوا فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ (34) أَمْ أَنزَلْنَا عَلَيْهِمْ سُلْطَانًا فَهُوَ يَتَكَلَّمُ بِمَا كَانُوا بِهِ يُشْرِكُونَ (35) وَإِذَا أَذَقْنَا النَّاسَ رَحْمَةً فَرِحُوا بِهَا ۖ وَإِن تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ إِذَا هُمْ يَقْنَطُونَ (36) أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّ اللَّهَ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ وَيَقْدِرُ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ (37) فَآتِ ذَا الْقُرْبَىٰ حَقَّهُ وَالْمِسْكِينَ وَابْنَ السَّبِيلِ ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يُرِيدُونَ وَجْهَ اللَّهِ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ (38) وَمَا آتَيْتُم مِّن رِّبًا لِّيَرْبُوَ فِي أَمْوَالِ النَّاسِ فَلَا يَرْبُو عِندَ اللَّهِ ۖ وَمَا آتَيْتُم مِّن زَكَاةٍ تُرِيدُونَ وَجْهَ اللَّهِ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُضْعِفُونَ (39) اللَّهُ الَّذِي خَلَقَكُمْ ثُمَّ رَزَقَكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يُحْيِيكُمْ ۖ هَلْ مِن شُرَكَائِكُم مَّن يَفْعَلُ مِن ذَٰلِكُم مِّن شَيْءٍ ۚ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ (40) ظَهَرَ الْفَسَادُ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ بِمَا كَسَبَتْ أَيْدِي النَّاسِ لِيُذِيقَهُم بَعْضَ الَّذِي عَمِلُوا لَعَلَّهُمْ يَرْجِعُونَ (41)
الصفحة Page 408
(33) Kuma idan cũta ta shãfi mutãne, sai su kirãyi Ubangijinsu, sunã mãsu mai da al'amari gare Shi, sa'an nan idan Ya ɗanɗana musu wata rahama daga gare Shi, sai gã wani ɓangare daga gare su sunã shirki da Ubangijinsu.
(34) Dõmin su kãfirta dl abin da Muka bã su. To ku ji dãɗi kaɗan Sa'an nan zã ku, sani.
(35) Kõ Mun saukar da wani dalĩ li a gare su? Shi kuwa yanã magana da abin da suka kasance sunã shirkin da shi?
(36) Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita kuma idan cũta ta sãme su, sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, sai gã su sunã yanke ƙauna,
(37) Shin, kuma ba su gani ba cẽwa Allah na shimfida arziki ga wanda Yake so kuma Yanã ƙuntatãwa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin ĩmãni.
(38) Sabõda haka ka bai wa zumu hakkinsa da miskĩnai da ɗan hanya, wannan shĩ ne alhẽri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan sũ ne mãsu sãmun babban rabo.
(39) Kuma abin da kuka bãyar na riba dõmin ya ƙãru a cikin dũkiyar mutãne to, bã zai ƙãru ba, a wurin Allah. Kuma abin da kuka bãyar na zakka, kanã nufin yardar Allah to (mãsu yin haka) waɗancan sũ ne mãsu ninkãwa (ga dũkiyarsu).
(40) Allah ne Wanda Ya halitta ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku, sa'an nan Ya rãyar da ku. Ashe, daga cikin abũbuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga waɗannan ahũbuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya ɗaukaka bisa ga abin da suke yi na shirki.
(41) ¥arnã tã bayyana a cikin ƙasa da tẽku, sabõda abin da hannãyen mutãne suka aikata. Dõmin Allah Ya ɗanɗana musu sãshin abin da suka aikata, ɗammãninsu zã su kõmo.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022