(84) "Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya a cikin mutãnen ƙarshe."
(85) "Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima."
(86) "Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu."
(87) "Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su."
(88) "A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi."
(89) "Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki."
(90) Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa.
(91) Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku.
(92) Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa?"
(93) "Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu?"
(94) Sai aka kikkife su a cikinta, su da halakakkun.
(95) Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya.
(96) Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma,
(97) "Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna."
(98) "A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu.
(99) "Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi."
(100) "Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta."
(101) "Kuma bã mu da abõki, masõyi."
(102) "Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai!"
(103) Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba.
(104) Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
(105) Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni.
(106) A lõkacin da ɗan'uwansu, Nũhu, ya ce musu, "Shin, bã zã ku yi taƙawa ba?"
(107) "Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce."
(108) "To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
(109) "Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu."
(110) "Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã."
(111) Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka?"