يس   سورة  : Yaseen


سورة Sura   يس   Yaseen
إِنَّ أَصْحَابَ الْجَنَّةِ الْيَوْمَ فِي شُغُلٍ فَاكِهُونَ (55) هُمْ وَأَزْوَاجُهُمْ فِي ظِلَالٍ عَلَى الْأَرَائِكِ مُتَّكِئُونَ (56) لَهُمْ فِيهَا فَاكِهَةٌ وَلَهُم مَّا يَدَّعُونَ (57) سَلَامٌ قَوْلًا مِّن رَّبٍّ رَّحِيمٍ (58) وَامْتَازُوا الْيَوْمَ أَيُّهَا الْمُجْرِمُونَ (59) ۞ أَلَمْ أَعْهَدْ إِلَيْكُمْ يَا بَنِي آدَمَ أَن لَّا تَعْبُدُوا الشَّيْطَانَ ۖ إِنَّهُ لَكُمْ عَدُوٌّ مُّبِينٌ (60) وَأَنِ اعْبُدُونِي ۚ هَٰذَا صِرَاطٌ مُّسْتَقِيمٌ (61) وَلَقَدْ أَضَلَّ مِنكُمْ جِبِلًّا كَثِيرًا ۖ أَفَلَمْ تَكُونُوا تَعْقِلُونَ (62) هَٰذِهِ جَهَنَّمُ الَّتِي كُنتُمْ تُوعَدُونَ (63) اصْلَوْهَا الْيَوْمَ بِمَا كُنتُمْ تَكْفُرُونَ (64) الْيَوْمَ نَخْتِمُ عَلَىٰ أَفْوَاهِهِمْ وَتُكَلِّمُنَا أَيْدِيهِمْ وَتَشْهَدُ أَرْجُلُهُم بِمَا كَانُوا يَكْسِبُونَ (65) وَلَوْ نَشَاءُ لَطَمَسْنَا عَلَىٰ أَعْيُنِهِمْ فَاسْتَبَقُوا الصِّرَاطَ فَأَنَّىٰ يُبْصِرُونَ (66) وَلَوْ نَشَاءُ لَمَسَخْنَاهُمْ عَلَىٰ مَكَانَتِهِمْ فَمَا اسْتَطَاعُوا مُضِيًّا وَلَا يَرْجِعُونَ (67) وَمَن نُّعَمِّرْهُ نُنَكِّسْهُ فِي الْخَلْقِ ۖ أَفَلَا يَعْقِلُونَ (68) وَمَا عَلَّمْنَاهُ الشِّعْرَ وَمَا يَنبَغِي لَهُ ۚ إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ وَقُرْآنٌ مُّبِينٌ (69) لِّيُنذِرَ مَن كَانَ حَيًّا وَيَحِقَّ الْقَوْلُ عَلَى الْكَافِرِينَ (70)
الصفحة Page 444
(55) Lalle, 'yan Aljanna, a yau, sunã cikin shagali, sunã mãsu nishãɗi.
(56) Sũ da mãtan aurensu sunã cikin inuwõwi, a kan karagai, sunã mãsu gincira.
(57) Sunã da, 'ya'yan itãcen marmari a cikinta kuma sunã sãmun abin da suke kiran a kãwo.
(58) "Aminci," da magana, daga Ubangiji Mai jin ƙai.
(59) "Ku rarrabe dabam, a yau, yã kũ mãsu laifi!"
(60) "Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, yã ɗiyan Ãdamu? Cẽwa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shĩ, maƙiyi ne a gareku bayyananne?"
(61) "Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya."
(62) "Kuma lalle haƙĩƙa, (Shaiɗan) yã ɓatar da jama'a mãsu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kunã yin hankali ba?"
(63) "Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance anã yi muku wa'adi da ita."
(64) "Ku shigẽ ta a yau, sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci."
(65) A yau, Munã sanya hãtimin rufi a kan bãkunansu, kuma hannãyensu su yi Mana magana, kuma ƙafãfunsu su yi shaidu da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
(66) Dã Mun so, dã Mun shãfe gani daga idãnunsu, sai su yi tsẽre ga hanya, to, yaya zã su yi gani?
(67) Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba zã su iya shuɗewa ba, kuma ba zã su komo ba.
(68) Kuma wanda Muka rãya shi, Manã sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, bã su hankalta?
(69) Ba Mu sanar da shi (Annabi) wãkã ba, kuma wãkã ba ta kamãta da shi (Annabi) ba. Shi (Al-ƙur'ãni) bai zama ba fãce tunãtarwa ce, da abin karãtu bayyananne.
(70) Dõmin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kãfirai.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022