(187) Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin waɗanda aka bai wa Littãfi, "Lalle ne kuna bayyana shi ga mutãne, kuma bã zã ku ɓõye shi ba." Sai suka jẽfarda shi a bãyan bãyansu, kuma suka sayi 'yan kuɗi kaɗan da shi. To, tir da abin da suke saye!
(188) Kada lalle ka yi zaton waɗanda suke yin farin ciki da abin da suka bãyar, kuma suna son a yabe su da abin da ba su aikatã ba. To, kada lalle ka yi zaton su da tsĩra daga azãba. Kuma suna da azãba mai raɗadi.
(189) Kuma ga Allah mulkin sammai da ƙasa yake. Kuma Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne.
(190) Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma'abũta hankali.
(191) Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. TsarkinKa! Sabõda haka Ka tsare mu daga azãbar wuta.
(192) "Ya Ubangijinmu! Lalle ne Kai, wanda Ka shigar a cikin wuta to, haƙĩƙa, Ka tozarta shi kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai.
(193) "Yã Ubangijinmu! Lalle ne mũ mun ji Mai kira yanã kira zuwa ga ĩmãni cẽwa, 'Ku yi ĩmãni da Ubangijinku.' Sai muka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Sabõda haka Ka gãfarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyãgun ayyukanmu daga gare mu. Kuma Ka karɓi rãyukanmu tãre da mutãnen kirki.
(194) "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu abin da Ka yi mana wa'adi (alkawari) a kan manzanninKa, kuma kada Ka tozarta mu a Rãnar ¡iyãma. Lalle ne Kai, bã Ka sãɓãwar alkawari."