(53) "Kuma bã ni kuɓutar da kaina. Lalle ne rai, haƙĩƙa, mai yawan umurni ne da mummũnan aiki, fãce abin da Ubangjina Ya yi na; rahama. Lalle Ubangjina Mai gãfara ne, Mai jin ƙai."
(54) Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi in kẽɓe shi ga kaina." To, a lõkacin da Yũsufu ya yi masa magana sai ya ce: "Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne, amintacce."
(55) Ya ce: "Ka sanya ni a kan taskõkin ƙasa. Lalle ne nĩ, mai tsarẽwa ne, kuma masani."
(56) Kuma kamar wancan ne Muka bãyar da ĩko ga Yũsufu a cikin ƙasa yanã sauka a inda duk yake so. Munã sãmun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma bã Mu tõzartar da lãdar mãsu kyautatawa.
(57) Kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi alhẽri ga waɗandasuka yi ĩmãni, kuma suka kasance mãsu taƙawa.
(58) Kuma 'yan'uwan Yũsufu suka jẽ, sa'an nan suka shiga a gare shi, sai ya gãne su, alhãli kuwa su, sunã mãsu musunsa.
(59) Kuma a lõkacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce: "Ku zo mini da wani ɗan'uwa nãku daga ubanku. Ba ku gani ba cẽwa lalle ne nĩ, inã cika ma'auni, kuma nĩ ne mafi alhẽrin mãsu saukarwa?"
(60) "Sa'an nan idan ba ku zo mini da shĩ ba, to, bãbu awoa gare ku a wurĩna, kuma kada ku, kasance ni."
(61) Suka ce: "Zã mu nẽme shi daga ubansa. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu aikatãwa ne."
(62) Kuma ya ce wa yaransa, "Ku sanya hajjarsu a cikin kãyansu, tsammãninsu sunã gãne ta idan sun jũya zuwa ga mutãnensu, tsammã ninsu, zã su kõmo."
(63) To, a lõkacin da suka kõma zuwa ga ubansu, suka ce: "Yã bãbanmu! An hana mu awo sai ka aika ɗan'uwanmu tãre da mu. Zã mu yi awo. Kuma lalle ne, haƙĩƙa mũ, mãsu lũra da Shi ne."