الانسان   سورة  : Al-Insaan


سورة Sura   الانسان   Al-Insaan
وَمِنَ اللَّيْلِ فَاسْجُدْ لَهُ وَسَبِّحْهُ لَيْلًا طَوِيلًا (26) إِنَّ هَٰؤُلَاءِ يُحِبُّونَ الْعَاجِلَةَ وَيَذَرُونَ وَرَاءَهُمْ يَوْمًا ثَقِيلًا (27) نَّحْنُ خَلَقْنَاهُمْ وَشَدَدْنَا أَسْرَهُمْ ۖ وَإِذَا شِئْنَا بَدَّلْنَا أَمْثَالَهُمْ تَبْدِيلًا (28) إِنَّ هَٰذِهِ تَذْكِرَةٌ ۖ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِ سَبِيلًا (29) وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمًا (30) يُدْخِلُ مَن يَشَاءُ فِي رَحْمَتِهِ ۚ وَالظَّالِمِينَ أَعَدَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا (31)
المرسلات Al-Mursalaat
وَالْمُرْسَلَاتِ عُرْفًا (1) فَالْعَاصِفَاتِ عَصْفًا (2) وَالنَّاشِرَاتِ نَشْرًا (3) فَالْفَارِقَاتِ فَرْقًا (4) فَالْمُلْقِيَاتِ ذِكْرًا (5) عُذْرًا أَوْ نُذْرًا (6) إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَاقِعٌ (7) فَإِذَا النُّجُومُ طُمِسَتْ (8) وَإِذَا السَّمَاءُ فُرِجَتْ (9) وَإِذَا الْجِبَالُ نُسِفَتْ (10) وَإِذَا الرُّسُلُ أُقِّتَتْ (11) لِأَيِّ يَوْمٍ أُجِّلَتْ (12) لِيَوْمِ الْفَصْلِ (13) وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الْفَصْلِ (14) وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (15) أَلَمْ نُهْلِكِ الْأَوَّلِينَ (16) ثُمَّ نُتْبِعُهُمُ الْآخِرِينَ (17) كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَ (18) وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (19)
الصفحة Page 580
(26) Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo.
(27) Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa (dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi.
(28) Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa.
(29) Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa.
(30) Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima.
(31) Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.
المرسلات Al-Mursalaat
(1) Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
(2) Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
(3) Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
(4) sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
(5) Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
(6) Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
(7) Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
(8) To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
(9) Kuma, idan sama aka tsãge ta.
(10) Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
(11) Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
(12) Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
(13) Domin rãnar rarrabẽwa.
(14) Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
(15) Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
(16) Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
(17) Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
(18) Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
(19) Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022