ابراهيم   سورة  : Ibrahim


سورة Sura   ابراهيم   Ibrahim
تُؤْتِي أُكُلَهَا كُلَّ حِينٍ بِإِذْنِ رَبِّهَا ۗ وَيَضْرِبُ اللَّهُ الْأَمْثَالَ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ (25) وَمَثَلُ كَلِمَةٍ خَبِيثَةٍ كَشَجَرَةٍ خَبِيثَةٍ اجْتُثَّتْ مِن فَوْقِ الْأَرْضِ مَا لَهَا مِن قَرَارٍ (26) يُثَبِّتُ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا بِالْقَوْلِ الثَّابِتِ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَفِي الْآخِرَةِ ۖ وَيُضِلُّ اللَّهُ الظَّالِمِينَ ۚ وَيَفْعَلُ اللَّهُ مَا يَشَاءُ (27) ۞ أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ بَدَّلُوا نِعْمَتَ اللَّهِ كُفْرًا وَأَحَلُّوا قَوْمَهُمْ دَارَ الْبَوَارِ (28) جَهَنَّمَ يَصْلَوْنَهَا ۖ وَبِئْسَ الْقَرَارُ (29) وَجَعَلُوا لِلَّهِ أَندَادًا لِّيُضِلُّوا عَن سَبِيلِهِ ۗ قُلْ تَمَتَّعُوا فَإِنَّ مَصِيرَكُمْ إِلَى النَّارِ (30) قُل لِّعِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا يُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُنفِقُوا مِمَّا رَزَقْنَاهُمْ سِرًّا وَعَلَانِيَةً مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِيَ يَوْمٌ لَّا بَيْعٌ فِيهِ وَلَا خِلَالٌ (31) اللَّهُ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَأَنزَلَ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَأَخْرَجَ بِهِ مِنَ الثَّمَرَاتِ رِزْقًا لَّكُمْ ۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ الْفُلْكَ لِتَجْرِيَ فِي الْبَحْرِ بِأَمْرِهِ ۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ الْأَنْهَارَ (32) وَسَخَّرَ لَكُمُ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ دَائِبَيْنِ ۖ وَسَخَّرَ لَكُمُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ (33)
الصفحة Page 259
(25) Tanã bãyar da abincinta a kõwane lõkaci da iznin Ubangijinta! Kuma Allah Yanã buga misãli ga mutãne, mai yiwuwã ne, sunã tunãwa.
(26) Kuma misalin kalma mummũnã kamar itãciya mummũnã ce, an tumɓuke ta daga bisa ga ƙasa, bã ta da wata tabbata.
(27) Allah Yanã tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni da magana tabbatacciya a cikin rãyuwar dũniya, da cikin Lãhira, Kuma Allah Yanã ɓatar da azzãlumai, kuma Allah Yanã aikata abin da Yake so.
(28) Shin ba ka lura ba da waɗanda suka musanya ni'imar Allah da kãfirci kuma suka saukar da mutãnensu a gidan halakã?
(29) Sunã ƙõnuwa a wutar jahannama, kuma tir da matabbatarsu.
(30) Kuma suka sanya wa Allah kĩshiyõyi, dõmin ɓatarwa daga hanyarSa, Ka ce: "Ku ji dãɗi, sa'an nan, lalle ne, makõmarku Wutar ce."
(31) Ka ce wa bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni su tsayar da salla kuma su ciyar daga abin da Muka azurtã su, a asirce da bayyane, daga gabãnin wani wuni ya zo, bãbu ciniki a ciki, kuma bãbu abõtaka.
(32) Allah ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar game da shi, daga 'ya'yan itãce arziki dõminku kuma Ya hõrẽ jirgin ruwa dõmin ya yi gudu a cikin tẽku da umurninSa, kuma Ya hõrẽ muku kõguna.
(33) Kuma Ya hõrẽ muku rãnã da watã sunã madawwama biyu, kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022